Shin nakasassu za su iya daina bara saboda tallafi?

Wasu nakasassu a jihar Legas Nijeriya
Image caption Gwamnatin jihar Legas ta nuna damuwa kan matsalar barace-barace a fadin jihar

Nakasassu 500 ne za su ci gajiyar tallafin kudade da kekuna da motocin guragu da sauran kayayyaki daga gwamnatin jihar Legas.

Za a bai wa ko wannensu tallafin Naira dubu dari daya ne.

Da yawa daga cikin masu cin wannan gajiya sun fito daga arewacin Nijeriyar ne.

Abdullahi Kabir Ahmed wani jami'n gwamnatin jihar Legas din ne da ya yiwa BBC karin bayani cewa, dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta dau wannna mataki shine don da shawo kan matsalar barace-barace a fadin jihar.

'' Ita dai gwamnatin Legas ta tsaya a kan cewa ba ta son jama'a su rika yin bara a cikin jihar, shi yasa aka ba su wannan tallafi don ya agaza musu su rika sana'o'i da ayyuna.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu nakasassun a Nijeriya sun ce dole ce ta sa suke yawon barace-barace

Alhaji Sama'ila shine sarkin makafin Agege a jihar Legas din da ya ce wannan tallafi ya kara musu karfin guiwa ta yadda za su iya bayar da tabbacin cewa za su daina barace-barace su kama sana'o'i.

Ya kuma ce da yake suna da kungiya mai tsari, wacce akwai masu sana'o'i, za su tattaru waje guda su yada wadannan manufofin gwamnatin na hana yin barar.

Malam Shu'aibu Audu wani gurgu ne da ya ce, ita bara dama ba don son ran su suke yi ba, kuma tun da suka samu wannan tallafi da yardar Allah za su bi dokokin gwamnati na nisantar barace-baracen.

Wasu rahotanni sun ce a duk fadin Nijeriya, jihar Legas ita ce ta fi yawan masu barace-barace.

Gwamnatin jihar ta kuma nuna damuwarta kan yadda ta ce irin rahotannin da ake kawo mata na yawan buge mabaratan da ababan hawa, da kuma fadawa hannun bata gari.

Labarai masu alaka