Mutane 36 sun hallaka a hadarin mota a China

Hadarin mota a kasar China Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu aikin ceto sun yi ta aiki cikin dare a inda hadarin ya faru

Wata babbar motar safa ta yi hadari ta yi karo da bangon hanyar karkashin kasa a kasar China, tare da hallaka mutane 36, da kuma jikkata 13.

Babbar motar ta bar birnin Chengdu a kan hanyarta da zuwa garin Luoyang a lokacin da ta yi hadarin a lardin Shaanxi provincekafin tsakar daren Alhamis.

Ana da gudanar da aikin ceto, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin hadarin ba.

Amma kuma munanan haduran kan hanya sun zama ruwan dare a kasar ta China.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kididdige cewa mutane 250,000 ne suka mutu sakamakon hadurran kan hanyar a kasar China a shekara ta 2013.

Labarai masu alaka