Ka'idojin shiga gasar "Hikayata" ta 2017

Gasar Hikayata ta BBC Hausa
Bayanan hoto,

Ranar Lahadi 10 ga watan Satumba za a rufe gasar "Hikayata" ta bana

"Hikayata" gasa ce ta gajerun kagaggun labarai wadda Sashen Hausa na BBC ke shiryawa don mata zalla. Wannan ne karo na biyu da ake shirya wannan gasa, da aka fara bara. Duk wadda take sha'awar shiga gasar za ta iya aiko da labarinta idan ta dace da ka'idojin shiga gasar da ke tafe:

1. Dole ne duk wani labarin da za a turo da nufin shiga gasar "Hikayata" ya cika wadannan sharuddan:

1.1Dole ne labarin ya kasance kagagge kuma gajere — ya kasance kalma 1,000 zuwa 1,500.

1.2 Wajibi labarin ya kasance mace ce ta rubuta shi.

1.3 Dole ne labarin ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, ya kuma bi ka'idojin rubutu.

1.4 Wajibi ne wadda za ta turo da labarin ta zama ita ce ainihin wadda ta rubuta shi; ba a yarda wata ta aiko da labarin da wata ko wani ta ko ya rubuta ba.

1.5 Mata biyu za su iya shigar da labari daya a gasar, amma kada su wuce haka.

1.6 Ba a yarda mace daya ta aiko da labari fiye da daya ba.

1.7 Wajibi ne rubutun ya kasance bai kunshi wasu kalmomi da suka shafi batsa, ko yabon ta'addanci, ko kuma bata wa yara ko wata jama'a suna ba.

1.8 Matakin da alkalai za su dauka kan cancantar labarin da aka tura shi ne na karshe. Ba za a iya kalubalantar hukuncin ba.

BBC za ta watsa wasu daga cikin labaran da aka zaba a shirye-shiryenta, kuma za ta yi hakan ne da izinin masu rubutun. Za kuma a iya wallafa wasu daga cikin labaran a wani littafi, wanda kawo yanzu ba a tabbatar da yadda zai kasance ba, kuma hakan zai dogara ne da amincewar BBC.

Ba tilas ba ne BBC ta watsa ko ta wallafa kowanne daga cikin labaran da aka turo.

2. Yadda za a turo labari

2.1 Za a aiko da labaran ne ta email zuwa ga: labari.bbchausa@bbc.co.uk tare da wadannan bayanai na mai aikowar:

  • Suna
  • Lambar waya
  • Adireshi
  • Adireshin Email
  • Gajeren tarihin mai aikowa
  • Gajeren bayani a kan labarin
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

2.2 Ba za a karbi duk wani labari da bai cika sharuddan da ke sama ba.

2.3 Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu su shiga wannan gasa ba.

2.4 Ba a yarda marubuta ukun da suka yi zarra a gasar bara su shiga ta bana ba.

3. An bude gasar ranar Lahadi 6 ga watan Agusta 2017.

4. BBC za ta yi amfani da bayanan sirrin masu shiga gasar ne kawai a harkokin da suka shafi wannan gasar. A karanta tsarin amfani da bayanan sirri na BBC domin samun karin bayani.

5. Za a rufe gasar da misalin karfe 11:55 na dare a agogon GMT, ranar 30 ga watan Satumba 2017. Ba za a amince da duk wani labari da aka aiko bayan wannan lokaci ba.

6. Wajibi ne duk labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta turo da shi, kuma ya dace da ka'idojin da aka shimfida. Kada labarin ya shiga hakkin wani (wanda ya hada da bayanan sirri), kuma kada a bata wa wani suna ko a aikata abin da ya sabawa doka. BBC ba za ta dauki alhakin duk wani abu da ka iya biyo bayan saba wa wadannan ka'idoji ba, kuma duk wadda ta turo labari ta amince cewa za ta wanke BBC daga duk wani ikirari da wani/wata zai/za ta yi sakamakon saba wa wannan ka'ida.

7. Idan aka zabi labari, to za a nemi wadda ta turo da shi ta cike wani fom wanda zai bai wa BBC damar watsa labarin, za kuma a iya gayyatar marubuciyar ta nadi labarinta domin a watsa. Idan BBC ta yanke shawarar wallafa littafi a kan labaran da aka zaba kuma, fom din zai ba ta damar sanya labarin a cikin littafin.

Wadanda suka zo ta daya da ta biyu da ta uku ne kawai za su samu kyauta, inda za a bayar da $2,000 da lambar yabo ga wadda ta zo ta daya; sai $1,000 da lambar yabo ga ta biyu; yayin da za a bai wa ta uku $500 da lambar yabo. Za kuma a ambaci sauran labaran da suka kayatar.

8. Duk wacce ta turo da labarinta, to ta amince da wadannan ka'idojin da aka shimfida.

9. Matakin Farko - Tantancewa

Ma'aunin da za a duba don tantance labaran zai kasance kamar haka:

  • Labari mai asali - ba wanda aka kwafa ba.
  • Kwarewa - labari mai jan hankali da kuma kayatarwa.
  • Bin ka'idojin nahawu da na rubutun Hausa.

10. Wasu kwararru ne za su tantance labaran bisa ma'aunin da aka zayyana a sama, sannan su zabi labarai 25.

Daga nan ne za a tura labaran da aka tantance ga alkalai domin su yanke hukunci. Za a sanar da wadanda aka zabi labaransu daga ranar 20 ga watan Oktoba.

11. Mataki na biyu - Alkalanci da fitar da wadanda suka yi nasara

11.1Alkalai za su karanta, sannan su tattauna a kan, labaran da aka tantance.

11.2 Za a tuntubi wadanda suka yi nasara daga 2 zuwa 3 ga watan Nuwamba.

11.3 Za a bayar da sanarwar wadanda suka yi nasara ranar 4 ga watan Nuwamba.

12. Hukuncin alkalan shi ne na karshe. Ba za a tuntubi wadanda ba su yi nasara ba, kuma ba za a mayar musu da amsa kan labaran da suka turo ba.

13. Mai yiwuwa BBC ta gayyaci wadanda suka yi nasara domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja. [BBC za ta dauki nauyin kudin mota da masauki wanda bai wuce kima ba. Wadanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba 'yan kasar ba ne].

14. BBC na da ikon soke ko cire dukkan labarin da ya saba wa wadannan dokokin.

15. BBC na da ikon sauya wadannan ka'idojin a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaben ko kuma alkalan. Idan hakan ta faru, za a sanar a wannan shafin na intanet: bbchausa.com.

16. An tsara wadannan ka'idojin ne bisa dokokin Ingila da Wales.