'Madrid da Barca na neman Paulo Dybala na Juventus'

Dybala Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dybala ya koma Juventus ne a shekarar 2015

Real Madrid tana magana da Juventus a asirce kan zawarcin dan wasan gaban kungiyar, Paulo Dybala, wanda Barcelona take nema, in ji Don Balon.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ba za ta iya sayen Philippe Coutinho daga Liverpool ba, idan har ta sayi dan wasan Borussia Dortmund, Ousame Dembele, kamar yadda wani dan jaridar Spain, Graham Hunter, ya shaida wa BBC.

Arsenal ta ce za ta sabunta kwantiragin Alexis Sanchez, inda za ta rika biyansa fam 300,000 a kowane mako wanda hakan zai sa ya zama dan wasan da ya fi albashi a gasar Firimiya, in ji jaridar Daily Mail.

Sai dai SFR Sport ta ruwaito cewa kocin kulob din Arsene Wenger ya ce "ba shi da kwarin gwuiwa sosai" kan ko dan wasan zai amince ya ci gaba da zama a Arsenal.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanchez ya koma Arsenal ne daga Barcelona

Kulob din Juventus yana zawarcin dan wasan Liverpool, Emre Can, a kan fam miliyan 23, in ji jaridar Daily Mirror.

Ita kuwa West Ham tana neman William Carvalho na kungiyar Sporting Lisbon ne a kan fam miliyan 27.1, kamar yadda jaridar Daily Telegraph ta wallafa.

Kocin Leicester City Craig Shakespeare ya ce hankalinsa a kwance yake yayin da ake daf da rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai, in ji jaridar Daily Star.

Shi ma kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ya bai wa zawarcin Danny Rose fifiko sosai, kamar yadda jaridar Daily Record ta bayyana.

Labarai masu alaka