Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Fitattun hotunan abin da ya faru a Afirka da sauran sassan duniya a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai wasan tsalle-tsalle da guje-guje daga kasar Afirka ta Kudu, Luvo Manyonga, na tsallaka da kofin zinaren da ya ci a gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da ake yi a Landan ranar Asabar. Shekaru hudu da suka gabata ya saba da wasu kwayoyi da ake kira "tik", amma yanzu yana neman kafa sabuwar bajinta ne.
Hakkin mallakar hoto Ferdinand Omondi/BBC
Image caption A ranar Litinin ne aka dauki hoton wadannan mazan 'yan kabilar Maasai a lokacin da suke gudanar da sana'arsu ta kitso, a wurin da ake kira "Engineer Maasai Salon". Wurin na kan daya daga cikin manyan titunan birnin Mombasa na kasar Kenya.
Hakkin mallakar hoto Ferdinand Omondi/BBC
Image caption "Sanar gyaran gashi da maza suke yi ba sabon abu ba ne a kasar Kenya, amma maza 'yan kabilar Masaai su caba ado suna kitso sabo abu ne".
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata ne wadannan mazan suka zauna a gefen hoton shugabannin kungiyoyin addinin na Muanda Nsemiare a hedikwatar 'yan sanda da ke Kinshasa. 'Yan sanda a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo na zargin kungiyar Bundu Dia Mayala da hannu a rikicin da aka yi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 12 a Kinshasa, babban birnin kasar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar ne dai, Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma yake murna da nasarar da ya yi bayan da ya sha da kyar bayan kuri'ar yankar kaunar, duk da cewa da farko an yi zaben cikin sirri. Jam'iyyun adawa na ganin an yi zaben asirri ne don wasu daga cikin 'yan majalisar na jam'iyyar ANC za su iya goyon bayansu a kan zargin cin hanci da ake wa shugaban, sai dai ya samu rinjaye da kuri'a 198, yayin da 'yan hamayya suka samu 177.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mutum wanda yake daya daga cikin miliyoyin mutanen Kenya da suka kada kuri'arsu a babban zaben kasar da aka yi ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun da sassafe ne mutane suka fara kafa layi har zuwa dare domin kada kuri'arsu, tun daga kan zaben shugaban kasa har zuwa kasa.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Laraba ne wasu masu zanga-zanga suka fito wasu yankunan kasar, bayan da babban jagoran 'yan adawa, Raila Odinga, ya yi zargin cewa anyi kutse a kwamfutocin zaben tare da jirkita sakamakon zaben don Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi nasara. Sai dai jami'an zaben sun yi watsi da zargin.
Hakkin mallakar hoto Anthonu Irungu/BBC
Image caption A ranar Alhamis ne John Paul Mwirigi yake murna da 'yan uwansa, bayan da ya zama dan majalisa mafi kankanta a Kenya. Dan shekara 23, dalibi ne a jami'a, inda zai wakilci wata mazaba a gabashin Meru, ya bayyana cewa, "Babban farin-cikina shi ne yadda mutanen mazabata suka gano cewa matashi zai iya jagorantarsu".
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan kasar Kenya na mayar da hankalinsu wajen kallon abin da ke wakana, a lokacin da hukumar zabe ke ci gaba da tattara sakamakon zaben kasar.