Cibiyoyin shan mayen da ke 'saya' wa 'yan kwaya mutunci

Insite Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cibiyar allurar sa maye ta farko a Kanada na kokarin ci gaba da aiki

Yayin da matsalar shan hodar iblis nau'in opioid ke bazuwa a fadin Amurka ta Arewa, birnin Vancouver na kasar Kanada ya zama ja gaba wajen yin mai dungurungum don magance shan kwaya - ta hanyar barin mutanen da suka jarabtu su sha su yi mankas.

Duk ranar biyan albashi a gabashin tsakiyar birnin Vancouver, mutane suna cike da nishadi. Bayan sun karbi kudaden tallafin rayuwa na wata-wata, mazauna yankin da dama sukan tudada zuwa kasuwa da ke ci a gefen tituna, inda masu sana'o'i ke sayar da kayayyaki kama daga faya-fayen DVD da aka haramta zuwa 'yan kayayyakin hannu.

Sai dai ba kawai a kasuwa ne, kudi ke musayar hannu ba. A kan tituna da rukunin gidajen da ke kunshe a yankin, hada-hadar kwaya na bunkasa, haka ma shaye-shaye fiye da kima.

"Kawai za ka zo aiki kullum, sai ka ga mutum ya mutu," a cewar Sarah Blyth, wata mai fadakarwa a tsakanin jama'a da ke gudanar da kasuwar. "Abin na da matukar ban takaici."

Hodar iblis wani bangare ne na rayuwar mutanen yankin Downtown Eastside.

A shekarar 1990, amfani da allura a tsakanin masu shaye-shaye a birnin Vancouver ya janyo "wata gawurtacciyar annoba ta kwayar cutar kanjamau da aka taba gani ta bazu a wani yanki daban da Kudu da Saharar Hamada," a cewar Dr. Thomas Kerr mai bincike a kan cutar kanjamau.

Wannan al'amari ya kai ga bude cibiyar sanya ido kan allurar sa maye ta farko a Amurka ta Arewa, mai suna Insite. A yanzu an samu yaduwar annobar shan hodar sa maye ta opioid, kuma unguwar Downtown Eastside ta zamo wata cibiyar kyankyasar hanyoyin magance matsalar shan kwaya wadda ba a saba gani ba.

Image caption Taswirar cibiyoyin allurar sa maye a tsakiyar birnin Vancouver

Cibiyar Insite, wadda ake allurar sa maye tana nan a tsallaken kasuwa. Kuma tun bayan bude ta a shekara ta 2003, cibiyar ta zama jiki ga al'ummar tsakiyar birnin Vancouver.

Cibiyar tana da sarari, ga haske ya dallare cikinta mai siffar asibiti - kwata-kwata ta sha bamban da irin yanayin da aka saba ganin 'yan kwaya da kan yi cukus a lungunan unguwa cikin kazanta. A watan Yunin 2017 kadai, dakin yin allurar sa maye na cibiyar Insite ya samu ziyara har kimanin 10,600.

A tsawon shekara 14, ba ko mutum daya da ya mutu sakamakon shan kwaya fiye da kima a wannan waje ko ma wata cibiya da ake sa ido kan masu allurar sa maye a Vancouver.

Daraktan da ya assasa cibiyar, Chris Buchner ya ce ginin ya samar da "mutunci ga mutanen da ba a ganin kimarsu a rayuwar yau da gobe".

Mr Buchner ya fara aikinsa ne a matsayin dan fafutukar takaita kwayar cutar kanjamau a Montreal, kuma ya fara aiki a cibiyar Insite don kula da "masu matsalar shan kwaya, ba ta fuskar masu aikata laifi ko marasa tarbiyya ba, amma a matsayin wani al'amari na lafiya da zamantakewa".

Ana barin masu zuwa cibiyar su dirka wa kansu allurar sa maye, yayin da ma'aikaciyar jinya ko likita ke tsaye yana kula.

Insite na tallafa wa 'yan kwaya wajen samun sauran al'amuran rayuwa kamar gidaje da kula da lafiyar masu larurar kwakwalwa da samar da aikin cire dattin ciki da nufin taimaka wa mutane su kasance cikin tsafta.

Image caption Kayan maye irin daban-daban a wata cibiya da ke Vancouver

Gomman mukaloli da suka hadar da British Medical Journal da the Lancet, sun mara wa ikirarin cibiyar Insite baya da cewa irin wadannan dabaru sun rage yaduwar cuta da kawo hargitsi a cikin jama'a kuma suna iya taimaka wa matuka wajen karfafa gwiwar mutane su kaurace wa shan kwaya don kansu.

Wannan bincike ya taimaka wajen bijiro da sha'awar bude makamantan wannan cibiya a fadin Amurka ta Arewa. Ya zuwa yau, Hukumomin lafiya a Kanada sun ba da lasisi 16 ga cibiyoyin allurar sa maye a fadin kasar. Shi ma birnin Seattle na Amurka yana fatan bude wani dan sha-ka-tafi.

Masu sukar lamiri sun zargi cibiyar Insite da sallamawa a kan masu jarabar shan kwaya, sai dai daraktan sha-ka-tafin na yanzu Dr Mark Lysyshyn ya yi imani cewa akasin haka ne ke faruwa.

"Taimaka wa mutane ne lokacin da suke bukatar haka, a taimaka musu su ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin da suke da zabin neman magani ko kuma yi musu aikin cire dattin ciki," a cewarsa.

Sai dai, bazuwar kwayar fentanyl, wata muguwar kwayar opioid wadda ta fi karfin hodar iblis sau kimanin 50 zuwa 100, ta mayar da allurar sa maye daga wani aikin gwajin likitanci zuwa tilas.

Babu wani wuri da wannan al'amari ya fi kamari kamar Vancouver. An yi kiyasin cewa mutum 430 ne suka mutu sakamakon shan maye fiye da kima a birnin cikin wannan shekara, kusan ninkin mace-macen da aka samu bara.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Mutum kan yi wa kanshi allurar sa maye ya yi mankas a cibiyar

Sai dai, Blyth ta tuna lokacin da abubuwa suka fara daukar wani salo, a kusan shekara ta 2016. Ko da yake, shan maye fiye da kima a kullum matsala ce da ake samu a lungunan bayan kasuwa, ta ce abin ya kai ga kullum safiya sai an samu sabuwar gawa.

"A ko'ina mutane ne kwance sharaf-sharaf," in ji ta.

Misis Blyth ta samu horo kan yadda za ba wa mutum maganin Naloxone, wanda ke hana kwayar opioid da aka sha fiye da kima yin tasiri a jiki, lokacin da take aiki a wata cibiyar marasa galihu da ke yankin. Kafin ta samu kanta a cibiyar Insite inda take ba da maganin a kullum.

A shekara ta 2016, ita da rukunin wasu 'yan sa-kai sun kafa wata kungiyar hana shan kwaya fiye da kima don sa ido kan wata cibiyar yin allurar sa maye da ke tsakanin titin kasuwar da kuma wani kwararo, a wani abu da yanzu ake kira "Area 62". Ta taimaka wajen horas da mutane yadda za su yi amfani da maganin Naloxone, nan fa aka fara turmutsutsu don sayen maganin.

Image caption Sarah Blyth tsaye a wajen kasuwar Downtown Eastside

Ba kamar cibiyar Insite ba, wadda gwamnati ta yi mata togaciya ta musammam a dokokin hana tu'ammali da kwaya na tarayya, Area 62 haramtacciya ce lokacin da ta fara aiki. 'Yan sanda sun kawar mata da kai har zuwa Kirsimetin 2016, lokacin da sashen kula da lafiyar jama'a a Vancouver ya ba su lasisi.

Cibiyar hana shan kwaya fiye da kima tana gudanar da ayyukanta ne a cikin tantuna. Kuma akasarin jami'an sa-kan 'yan unguwar ne, wadanda ko dai 'yan kwaya ne su kansu ko kuma 'yan'uwansu na sha.

Wata 'yar unguwar Robin Macintosh, wadda dan'uwanta ke shan maye fiye da kima a 1993, ta ce aikin sa-kan ya yi rayuwarta fa'ida. Ta kirga daruruwan mutanen da ta taimaka wa rayuwarsu.

A tsallaken titi

Can a gangaren titi daga Area 62 daya daga cikin rumbunan hodar iblis ne mafi tsaro a birnin. Sai dai, wajen ba maboyar dillalan kwaya ba ne. Maimakon haka, sha-ka-tafi ne mai suna Providence Crosstown, cibiyar lafiya guda a Kanada da take samar da hodar iblis ga masu jarrabar shan kwaya.

Ko da yake, wasu likitoci a Burtaniya da wasu yankuna a Turai suna rubuta wa 'yan kwaya hodar iblis mafi inganci, sha-ka-tafin Crosstown shi ne cibiya daya tilo a Amurka ta Arewa da ke taimaka wa masu jarabar shan kwaya samun caji. An fara shirin ne a shekara ta 2009, kuma cibiyar tana da adadin mutum 130 da ke karbar kwaya.

'Ina samun hodar iblis dina daga inshorar lafiya'

Daya daga cikin wadannan mutane shi ne Russell Cooper. Wani jibgege ne sanye da falmaran, idan ka gan shi tamkar dan dambe, amma mai larurar shan kwaya ne da ke da taushin murya, ya kuma ce ya fahimci dalilin da ya sa mutane ka iya nuna rashin amincewarsu ga wannan hanyar magani mai cike da takaddama.

Image caption Russell Cooper ya ce shan hodar iblis daga asibiti ya taimaka masa zama mutum inda a yanzu har yake koyar da yara kan illar shan kwaya

"Ba na zarginsu. Don me za a yi amfani da harajin da suka biya na daloli don kawai wasu su yi caji?" ya fada bayan ya afa 'yar safe.

"Abin da kawai zan iya ce musu shi ne jarabar shan kwaya, gagarumin abu ne."

Mista Cooper ya ce tsawon shekara 30 kenan yana shan hodar iblis, tun bayan dandana ta karon farko a gidan yari.

Takan sa shi ya ji dadi - yana son ta, kuma abokansa suna amfani da ita. Sai dai idan ta sake shi, sai jikinsa ya rika karkarwa yana gumi, abu guda kawai da ke ransa - ina zai samu hodar iblis.

Lokacin da fito daga gidan yari, sai ya fara dillancin kwaya don samun kudin shan hodar iblis. Ya rasa damar rikon dansa inda ya koma gidan gajiyayyu da rayuwa. Ya yi kokarin daina shan hodar ta hanyar shan kwayar methadone sau da dama, a wani lokaci yakan shafe tsawon shekara daya ko biyu ba tare da ya sha ba.

Cooper na daga cikin mutane mafi dacewa da irin wannan shiri, a cewar Dr Scott MacDonald, babban likita a sha-ka-tafin Crosstown. Rubuta wa mutanen da suka kamu don su sha hodar iblis shi ne mataki na karshe ga mutanen da suka yi kokarin bari sau da dama a baya.

Mista Cooper ya yi imani shirin ya kubutar da rayuwarsa.

Abu daya da fi kauna game da shirin shi ne sake hada shi da dansa dan shekara 12.

Sai dai, duk da adadin shirye-shiryen kula da mutanen da suka jarabtu a Vancouver, karuwar mace-mace masu da alaka da kwayar fentanyl na nufin jami'an lafiya a kullum sun makaro.

"Sai ka ji tamkar ba wata hanya ce mai bullewa ba a wasu lokuta," a cewar Mista Buchner.

Labarai masu alaka