Sojin Nigeria 'sun kai samame' ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya

40902232 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisar Dinkin Duniya na da sansanoni da dama a Maiduguri inda take bai wa 'yan gudun hijira tallafi

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarun tsaron Nijeriya sun kai samame kan daya daga cikin ofisoshinta a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka gudanar da bincike ba tare da izini ba.

Wata mai magana da yawun Majalisar ta fada wa BBC cewa binciken, wanda aka shafe tsawon sa'a uku ana yi, an kaddamar da shi ne da sanyin safiyar ranar Juma'a a birnin Maiduguri.

Majalisar Ɗinkin Duniya na da yawan jami'ai a arewa maso gabashin Najeriya, inda suke bayar da tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Sai dai ta ce ba ta san dalilin da ya sa jami'an tsaron suka bincike daya daga cikin sansanonin, inda gomman ma'aikatan ke aiki da kwana ba.

Majalisar Duniya ta nemi hukumomin Najeriya cikin gaggawa su ba ta amsa kan dalilinsu na yin haka, ko da yake, ya zuwa yanzu ba su ce uffan ba.

Ɗaya daga cikin dalilan da mai yiwuwa ya janyo binciken, shi ne jita-jitar da alama ke zagayawa a Maiduguri cewa shugaban Boko Haram na samun mafaka a wani waje da ake kira - Red Roof, wanda suna ne na sansanin Majalisar Ɗinkin Duniyar.

Ta bukaci ma'aikatanta 'yan asalin yankin su yi aikinsu daga gida a ranar Juma'a sakamakon faruwar lamarin.

Ta kuma ce ta sauke jiragen helikwaftanta da ke samar da ayyukan agaji ga sansanonin da ke da nisa a matsayin wani mataki na riga-kafi.

Labarai masu alaka