'Liman ya ba da umarnin dukan wadanda ba sa sallah'

Masallaci a Siwtzerland Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu gabatar da kara a Switzerland sun tuhumi wani limamin addinin Musulunci, dan asalin kasar Habasha, wato Ethiopia, bisa zargin cewa ya sa a rika dukan Musulmin da ba sa sallah a garin da yake.

Limamin ya kuma ya bayar da umarnin a kashe su idan sun ki yarda su yi sallar.

An ce mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, ya yi kalaman ne a yayin wata huduba a wani masallaci a birnin Winterthur a shekarar da ta wuce.

Ana kuma zarginsa da samun wasu hotuna na yadda ake aiwatar da mummunan kisan-gilla, wadanda ya bai wa wasu mutane a shafin Facebook.

Masu gabatar da karar na neman a daure shi tsawon wata 18, sannan a kore shi daga Switzerland har shekara 15 nan gaba.

Labarai masu alaka