Adikon Zamani kan matsalar fyade
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda wani ya yi wa 'yar makwabcinsa fyade

  • Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yigame da matsalar fyaden, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Ko wacce wayewar gari, sai an samu labarin aikata fyade a wani waje. Abin ya zama ruwan dare ta yadda fushinmu da babatunmu ba sa wani tasiri.

Abin har ya zama cewa mutane ba sa kaduwa sosai yanzu idan suka ji labarin fyade.

Idan kuwa abin ya shafi yara kanana ne, sai dai mu girgiza kai kawai mu ce Allah ya sauwake.

Muna tambayar kanmu ko me ya sa hakan? Muna tambayar kanmu dalilin da ya sa fyade ya zama ruwan dare a yanzu?

Muna tambayar ko me ya sa yaranmu ba su tsira ba yanzu ko da a cikin gidajenmu yayin da muka bar su da 'yan uwanmu?

Wa za a zarga? Shin hakan na nufin rashin mayar da hankalin iyaye kan sha'anin 'ya'yansu na sa a dinga cutar da yaran ta hayar lalata da su ba tare da sanin iyayen ba?

Na hadu da wata baiwar Allah mai suna Asabe a Kaduna. Wani makwabcinsu dan shekara 38 ne ya yi mata fyade. Mahaifiyarta ta gaya min cewa sun matukar amincewa da wannan mutum.

Ta sawa ranta cewa shi mutum ne mai son yara shi ya sa ba ta taba kawo komai a ranta ba. A takaice ma har a lokacin da ya fara cin zarafin 'yar tata ba ta zarge shi da komai ba, sai da wata makwabciyarta ta jawo hankalinta kan yada halayyar 'yar ke sauyawa da kuma irin jita-jitar da ake yadawa a unguwar.

Da na tambayeta ko ya aka yi ba ta lura ba, sai ta ce min hankalinta ya dauku wajen ganin ta wadata 'ya'yanta da abin da za su rayu na bangaren ci da sha da sutura.

Ina taya iyayen yaran da aka yi wa fyade jaje sosai. Da wahala kwarai mutum ya gane irin halin bakin cikin da suke samun kansu a ciki a yayin da suka gane cewa an zalunci 'ya'yansu.

Babban abin bakin cikin ma shi ne idan har wanda ya aikata hakan dan gida ne.

Me ya sa ake samun karuwar yi wa yara fyade? Hukumomi ne ba sa yin abin da ya dace don ganin an yi adalci?

Masu fyade nawa aka kai kotu aka kuma yanke musu hukunci?

Na yi tattaunawa da Beelo wani matashi dan shekara 16 wanda wasu mutum biyu suka tare shi a wajen wata liyafa suka yi masa fyade a Kaduna.

Ya ce minan yi masa hakan ne a wani kebantaccen waje.

Duk da cewa hukuma ta kama wadanda suka aikata masa wannan aiki, amma ba su dauki wani dogon lokaci ba a hannun 'yan sanda sai aka sallame su.

Wannan ne abin da yake yawan faruwa in ji kwamishinar mata ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, inda ta ce ta gwammace ta mika batun masu fyade ga Rundunar Tsaro ta Civil Defence a maimakin 'yan sanda, saboda a cewarta su ba a iya juya su sosai kamar 'yan sanda.

Image caption A baya-bayan nan ma mata sun yi zanga-zanga kan yawaitar fyade a Kano

Na yi wa kakain 'yan sanda na jihar Kaduna tambayar ko me ya sa hakan? Sai ya kafe kai da fata cewa ana bin duk matakan da suka kamata wajen gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin.

Sai dai yayin da ake ci gaba da takaddama kan ko 'yan sanda da kotu ba sa abin da ya dace, ana ta ci gaba da samun yawaitar cin zarafin mutane ta hanyar fyade, ita kuma al'umma ta yi gum da bakinta, wadanda ke samun kansu kuma cikin wannan hali suna ci gaba da boye wa duniya halin da suke ciki saboda tasirin al'ada.

Me zai sa mu dinga kyamatar wadanda aka yi wa fyade kan alifin da ba nasu ba?

Ni a ganina babu hankali sam ga al'umma ta dinga nuna kyama ga wadanda aka yi wa fyade, musamman mata matasa, bayan su wadanda suka yi fyaden suke rayuwarsu kalau kamar ba su aikata wani mummunan abu ba.