Mutane 37 sun hallaka a hadarin jirgin kasa a Masar

Kasar Masar Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hadarin shine mafi muni a kasar Masar din tun bayan na watan Nuwambar shekara ta 2013

Wasu jiragen kasan fasinjoji sun yi karo a arewacin kasar Masar, tare da hallaka akalla mutane 37 da jikkata fiye da 120, kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana.

Tarago da dama ne suka kauce sakamakon hadarin wanda ya faru a birnin Askandariya mai tashar jiragen ruwa.

Rahotanni sun ce daya daga cikin jiragen kasan ne ya tsaya saboda matsalar inji da ya samu.

Sai dai ministan sufuri na kasar Hisham Arafat ya dora alhakin hadarin da ''kuskuren dan adam''.

Daya daga cikin jiragen kasan ya taso ne daga birnin Alkahira, kana dayan ya taso daga Port Said, inda daga bisani suka yi taho mu gama.

Wata mata da ke yankin da hadarin ya faru ta ce tana tsaye a saman dakinta lokacin da ta hangi hadarin jiragen.

" Sun tashi sama inda suka yi kamar dalar gyada a lokacin da suka yi taho mu gama din. Na fara ihu daga saman daki don mutane su farga su gudu,'' ta ce.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Har yanzu ba a gano musabbabin abkuwar hadarin ba

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya bayar da umarnin a gudanar da binciken musabbabin hadarin, kana gwamnati ta yi alkawarin biyan diyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.

A shekara ta 2013, gwamman mutane ne suka hallaka, lokacin da wani jirgin kasa ya yi karo da wata motar safa, da sauran ababan hawa a kudancin birnin Alkahira.

Hadarin jirgin kasa mafi muni da aka shaida a kusa da babban birnin ya faru ne a shekara ta 2002, lokacin da gobara da tashi a cikin jirgin ta hallaka mutane fiye da 370.

Labarai masu alaka