Nigeria: An kai wa 'yan sanda hari kusa da coci a Anambra

'Yan bindiga sun bude wuta a kan 'yan sanda masu sintiri
Image caption 'Yan sandan Najeriya sun ce ba a kai wa coci hari ba

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Anambra, ta ce ta damke daya daga cikin 'yan bindigar da suka bude wuta kan wasu 'yan sanda da ke sintiri a kusa da wani coci a birnin Onitcha na jihar Anambra.

An dai ce 'yan sandan na sintiri lokacin da wasu samari a kan babur suka bude musu wuta, a inda suka raunata dan sanda guda daya.

Kuma yanzu haka dan sanda na asibiti yana jinya.

Sai dai rundunar ta musanta labarin da ake yadawa, cewa wai 'yan bindigar sun kashe dan sanda da farar hula daya.

Sannan kuma rundunar ta ce babu gaskiya cewa 'yan bindigar sun kai wa cocin hari ne.

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka bude wa wasu masu bauta a coci wuta, a inda suka kashe mutane 11, a kauyen Ozubulu da ke jihar ta Anambra.