'Mutane rabin miliyan ke fama da Kwalara a Yemen'

Wani yaro da ya kamu da cutar kwalara, a kwance a asibitin birnin Sanaa (7 August 2017) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fiye da kashi 99 na wadanda suka kamu da cutar ne na cikin mawuyacin hali

Adadin wadanda suka kamu da cutar Kwalara, ya kai 500,000, tun bayan kasar Yemen ta fada mummunan yaki, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana.

A kalla mutum 1,975 ne suka rasa rayukansu, tun bayan barkewar cutar mai nasaba da rashin tsaftataccen ruwan sha tun a watan Afrilun bana.

Hukumar WHO ta ce mutanen da suka kamu da cutar na samun sauki, amma kuma a kalla mutum 5000 na kumawa da ita a ko wacce rana.

Cutar na kara yaduwa ne sakamakon rashin tsaftataccen ruwan sha, da tsaftar muhalli a yankunan da ake tashin hankali a kasar ta Yemen.

Fiye da mutum miliyan 14 ne suke fama da rashin ruwa mai inganci, da zama cikin kazantar tarin bola da ba a samun kwashewa saboda yaki.

Rashin kyawun muhalli, da ruwan sha, da abinci mai gina jiki na daga cikin matsalolin da suke kara yada cutar Kwalara.

Yawancin wadanda suka kamu da cutar ana ganewa ta farat daya, yayin da wasu ba a saurin ganewa har sai ta ci karfinsu a karshe kuma su mutu.

Ma'aikatar lafiya a Yemen na cikin wani yanayi na rashin kayan amfani, da magunguna da sauransu, shekara biyu da aka shafe ana yaki a kasar tsakanin magoya bayan gwamnati da 'yan tawayen Houthi mabiya darkar shi'a ya sake daidaita kasar.

Kuma tun fara yakin kasar lamuran kiwon lafiya suka kara munana, barkewar cutar Kwalara dai ita ce babbar da aka taba gani a duniya.

WHO ta kara da cewa rashin isasshen magani da kayan bukata na asibiti, ya janyo matukar koma baya a bangaren kiwon lafiya a kasar, kusan ma'aikatan sa kai 30,000 ne ke aiki ba tare da an biya su albashinsu na wata da watanni ba.

Babban jami'in hukumar lafiya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ma'aikatan agaji na aiki cikin mawuyacin hali, baya ga rashin biyan albashi rayuwarsu na cikin barazana.

Dubban mutane ba su da lafiya, amma babu isassun gadaje a asibitoci da za a kwantar da su, ba ruwan sha babu kuma magani.

Likitocin da jami'an lafiya su ne kashin bayan bangaren lafiya, to amma saboda rashin samun kulawa wasu daga cikin likitocin sun gwammace komawa inda suka fito.

Dr Tedros ya kara da kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da juna a kasar Yemen, su koma teburin sulhu tare da aiki da hanyoyin siyasa dan kawo karshen rikicin.

Labarai masu alaka