An tsige shugaban majalisa a Nigeria

Gwamnan jihar Edo a kudancin Najeriya Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Godwin Obaseki Gwamnan Jihar Edo

Majalisar Dokokin jihar Edo a Najeriya ta tsige shugaban majalisar jihar Mista Justin Okonoboh, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

A ranar Litinin ne aka tumbuke Mista Justin yayin wani zama a zauren majalisar da ke birnin Benin City.

Sai dai jagoran majalisar ya ce cirewar da aka yi masa ta saba wa doka, kuma har ma ya ba da umarnin dakatar da 'yan majalisar da suka tsige shi.

'Yan majalisar sun ce daya daga cikin dalilan da suka sa su daukar matakin shi ne "yadda ya sa aka rufe majalisar na tsawon kwanaki don ya halarci bikin kammala karatun dansa a kasar Amurka."

Har ila yau sun zargi Mista Justin da saba wa doka wajen bayar da kwangiloli da sauransu.

Sai dai ya musanta duka zarge-zargen.

An maye gurbinsa ne da Kabiru Adjoto, kamar yadda kamfanin na NAN ya ce.

Kuma sabon shugaban majalisar ya fito ne daga mazabar Akoko-Edo I.

Labarai masu alaka