Ko masarautar Saudiyya na da hannu a batan 'ya'yanta?

Yarima Sultan bin Turki ne a tsakiyar hoton Hakkin mallakar hoto Hugh Miles
Image caption Yarima Sultan bin Turki ne a tsakiyar hoton

Shekara uku kenan da 'ya'yan masarautar Saudiyya su uku, da suke zaune a kasashen Turai suka yi batan dabo, kuma dukkansu na sukar lamirin gwamnatin kasar.

Akwai alamun dukkan ukun an tasa keyarsu gida Saudiyya, kuma tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsu ba.

Da sanyin wata safiya a ranar 12 ga watan Yuni 2003, aka tasa keyar daya daga cikin yarimomin wajen birnin Geneva.

Sunansa Sultan bin Turki, Yarima Abdulaziz bin Fahd ne ya gayyace shi cin abincin safe.

Abdulaziz ya roki Sultan ya koma gida Saudiyya, inda ya shaida masa za a magance kace-nacen da ake yi kan sukar da ya ke yi wa shugabannin kasar.

Amma sai Sultan ya ki amincewa da hakan, a wannan lokacin ne Yarima Abdul'aziz ya tashi daga inda suke zaune dauke da wayar salula da aka kira shi.

Jim kadan ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya, Sheikh Saleh al-Sheikh, da suke tare a dakin cin abincin shi ma ya fita, bayan dan lokaci sai wasu mutane sanye da wani bakin kyalle da suka rufe fuskokinsu da shi, suka shigo dakin, suka kuma lakadawa Sultan dan karen duka, aka kuma soka masa wata allura a wuyansa.

Sultan ya shiga wani yanayi na dimuwa da gushewar hankali, a hakan aka dauke shi har filin jirgin sama na Geneva, aka sanya shi a cikin wani jirgi wanda daman yana zaman jiran su ne.

Wannan labarin Yarima Sultan ne ya shaidawa wata kotu a kasar Switzaland shekaru da dama da suka wuce.

Mai magana da yawun Sultan, Eddie Ferreira na dakon dawowar maigidansa a Otal din da su ke zama a birnin Geneva, ya yi ta jiran dawowar uban gidan nasa amma shiru babu amo babu labari.

Daga nan ne kuma labarin ya fara shan banban, a lokacin da suka kasa samun masu tsaron lafiyarsa, sun yi kokarin kiran wayar salularsa nan ma ta ki shiga.

''Da rana kuma sai labarin ya sha banban, don kuwa wasu mutane na daban ne suka kawo mana ziyara,'' in ji Mista Ferreira.

Ya kara da cewa, ''Jakadan Saudiya a kasar Switzaland da manajan Otal din da muke, suka shaida mana kowa ya yi ta kansa.

Saboda a cewarsa, Yarima Sultan yana birnin Riyadh domin haka ba a bukatar mu a nan. "Abin da zuciyata ta tambaye ni shi ne me Yarima ya yi da 'yan uwansa suka masa duka tare da gusar masa da hankali da tasa keyarsa zuwa gida?" in ji Ferreira.'

Shekarun da suka gabata, da yariman ya zo duba lafiyarsa a kasar, ya yi Allah-wadai da dabi'ar take hakkin bil'adam da Saudiyya ke yi da kuma yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu tsakanin 'ya'yan masarautar da jimi'an gwamnati, ya kuma yi kiran a yi gagarumin garanbawul a masauratar.

Tun shekarar 1932, lokacin da sarki Abdulaziz da aka fi sani da Ibn Saud ya samar da kasar da a yanzu ake alfahari da ita a yankin gabas ta tsakiya, ake tafiyar da ita a tsarin mulkin gargajiya da ba sa son wani ya kawo musu wargi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarima Turki bin Bandar a lokacin ganawar sa da Firai ministan Pakistan a shekarar 2003

Yarima Turki bin Bandar daya ne daga cikin manyan 'yan sanda kasar, alhakin kula da masarautar na daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci da yake yi.

Amma rikicin gado da ya taso a masarautar Saudiyya ya janyo masa zaman kaso, bayan fitowarsa daga Kurkuku sai ya yi gudun hijira zuwa kasar Faransa.

A shekarar 2012 ne ya fara wallafa bidiyo a shafin Youtube inda yake kiran a yi sauye-sauye a Saudiyyar.

Shi ma abin da ya faru da Yarima Sultan ne ya kasance gare shi, inda hukumomin kasar suka yi ta masa dadin bakin ya dawo gida, a kuma kan hakan ne mataimakin ministan cikin gida Ahmed al-Salem ya kira shi ta wayar tarho, sai Yariman ya nadi tattaunawarsu tare da wallafawa a hafukan sada zumunta.

A cikin tattaunawar al-Salem ya shaidawa Turki cewa, ''Kowa na farin ciki tare da zuba idon ganin ka dawo gida, Allah ya yi maka albarka.''

Sai ya ce, ''Su na zuba idon ganin na dawo gida? Ina maganar wasikun da ku ke aiko min? Inda ku ke rubuta kalaman batanci ciki har da kira na ''kai dan karuwa, sai mun tilasta maka dawowa gida kamar yadda muka yi wa Sultan.''

''Ai babu wanda za mu bari ya taba ka, ka yarda dani ni dan uwanka ne.''

''Wasikun da ake aiko min daga ofishinka suke.''

Dukkan tattaunawar da suka yi sai da Turk ya wallafa su a shafukan sada zumunta a shekarar 2015.

''Kusan ko wanne wata sai ya kira ni a waya yana kokarin hilata ta na koma Saudiyya, daga baya kuma ban kara jin duriyarsa ba,'' in ji wani abokinsa Wael al-Khalaf.

Na shiga damuwa da kuma zargin wani abu ya faru da shi, daga bisani wata majiya daga wani babban jami'in Saudiyya ta sanar da ni ai Turki yana hannun masarautar, haka na nufin sun sace shi.

Na dauki lokaci mai tsawo ina son sanin halin da Turki ya ke ciki, sai daga bisani na ga wani rubutu da aka yi a wata jaridar kasar Moroko, cewa Turki na kan hanyar dawowa Faransa bayan wata ziyara da ya kai Moroko, a lokacin aka kama shi aka kulle shi a gidan kaso.

Bayanai sun nuna hukumomin Saudiyya ne suka tattauna da na Moroko suka bayar da izinin kama shi da tasa keyarsa zuwa gida da amincewar wata koton kasar.

Ba dai mu san abin da ya faru ga Turki bin Bandar ba, kafin bacewarsa ya bai wa abokinsa Wael wani littafi da ya rubuta, a cikin littafin ya yi wani ruhutu mai kama da wahayi.

Inda ya rubuta cewa, ''Ya kai dan uwana Wael, ka adana wannan bayanin da zan bar maka har sai an sace ni ko an hallaka ni sannan ka bayyana shi ga duniya. Saboda na san za a sace ni ko ma su hallaka ni, na san yadda suka take min hakki da sauran 'yan Saudiyya.''

Image caption Yarima Saud bin Saif al-Nasr

Kusan lokaci guda da bacewar Yarima Turki, wani yariman shi ma ya bace.

Yarima Saud bin Saif al-Nasr - ya kasance mai matsakaicin ra'ayi, yana kaunar yin wasan caca na Casino, yana kuma kaunar zama a manyan Otal.

A shekarar 2014 shi ma Saud ya fara wallafa rubuce-rubucen da yake yi a shafukan Twitter na nuna adawa da mulkin da ake yi a kasarsa.

Inda yake kiran a gurfanar da manyan jami'an gwamnatin Saudiyya a gaban shari'a, wadanda suka mara baya aka hambarar da shugaban kasar Masar Muhammad Morsi, a shekarun da suka wuce.

A watan Satumbar shekarar, abubuwan da Saud ke wallafawa suka kara zafafa.

Lamarin ya samo asali ne bayan wani yariman masarautar da ba a bayyana sunansa ba, ya rubuta wasiku guda biyu, yana kira a hambarar da mulkin Sarki Salman, ba tare da shawara ba kawai sai Saud ya danna alamun amincewa ya kuma zamo na farko a masarautar da ya aikata hakan.

Hukuncin wanda ya aikata hakan tsattsaura ne, don kuwa laifin cin amanar kasa ne ya rataya a kansa.

Bayan wasu kwanaki, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ''Ina kira ga al'umma su duba wasikun nan da idon basira, tare da matsa lambar ganin an aikata haka,'' daga wannan rana ba a kara ganin wani sako da ya wallafa ba.

Yarima Khaled bin Farhan

Bayan Saud, sai kuma Yarima Khaled bin Farhan, wanda ya yi hijira zuwa kasar Jamus a shekarar 2013- wanda ya yi amanna an yaudari Saud inda ya tashi daga Milan zuwa Rome don ganawa da wasu abokan kasuwancinsu daga kasashen Rasha da Italiya, da suke son bude reshen kamfaninsu a yankin Gulf.

An yaudare shi da hawa wani jirgi mai saukar ungulu daga Milan da nufin zai sauka a Rome, amma bai tsaya ko ina ba sai a birnin Riyardh, kamar yadda Yarima Khaled ya wallafa.

Ya kara da cewa an hada baki ne da hukumar leken asirin Saudiya don aiwatar da aikin.

''A halin da ake ciki baki daya Yarima Turki da Saud na garkame a gidan kaso, gidan kason ma na karkashin kasa da babu wanda ya san da shi,'' in ji Khaled.


Yarima Sultan, da aka yi masa daurin talala a Saudiyya na cikin mawuyacin hali, a farkon shekarar 2010 masarautar ta amince a fitar da shi kasar waje don neman magani saboda tsananin ciwon da yake fama da shi, an kuma kai shi asibitin Boston, da ke Massachusetts na Amurka.

Abin da ya yi wa masarautar a lokacin da yake kwance a asibitin Amurka, ya kuma shigar da karar masarautar a wata kotu da ke Switzerland, yana zargin Yarima Abdulaziz bin Fahd da Sheikh Saleh al-Sheikh da alhakin sace shi a shekarar 2003.

Lauyansa Ba'amurke Clyde Bergstresser, ya karbo sakamakon binciken lafiyarsa da aka yi a asibitin kwararru Sarki Faisal da ke Riyadh, inda aka kwantar da Sultan a ranar 13 ga watan Yulin 2003, sakamakon ya nuna an sanya masa wata siririyar roba a bakinsa don taimaka masa da yin nunfashi a lokacin da aka yi masa wata allura, sanadiyyar hakan wani bangare na jikinsa ya shanye.

Wannan shi ne karo na farko da wani dan masarautar Saudiyya ya gurfanar da wani gaban kotun kasashen yammacin duniya, abin mamakin kuma ya shigar da karar ne kan daya daga cikin mutanen gidansu.

Sai dai lauya Bergstresser ya yi korafin gwamnatin Switzerland ta nuna halin ko in kula kan batun.

''Babu wani abun a zo a gani da aka yi kan abin da ya faru a filin jirgin sama, ba a san su waye matuka jirgin ba? Shin me aka shirya jirgin zai yi a lokacin da ya sauka a kasar da kuma tashinsa zuwa Riyadh?

An sace yarima a kasar Switzerland, mutane za su yi tunanin ko hakan ya faru da sanin kasar da kuma amincewarta? Kai akwai tarin tambayoyi da ba mu da amsarsu,'' in ji Lauya Bergstresser.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A watan Janairun 2016, Yarima Sultan na zaune ne a wani hamshakin Otal da ke birnin Paris, kamar dan uwansa yarima Saud bin Saif al-Nasr a lokacin ne aka sace shi.

Yana shirin kai wa mahaifinsa ziyara, wani dan kasar Masar da ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin Saudiyya, a lokacin ne gwamnatin Saudiyya ta yi masa tayin za a kai shi a jirgi mai alfarma da kuma tayin za a duba lafiyarsa ta hanyar wani kwararren likita da masu tsaron lafiyarsa daga Amurka da Tarayyar Turai.

Duk da ya san abin da ya same shi a shekarar 2003, sai ya amince da su.

Biyu daga cikin mutanen da aka yi komai kan idonsu, sun bayyana yadda lamarin ya faru amma sun roki a sakaya sunan su saboda dalilai na tsaro.

"A lokacin da muka isa filin jirgi, sai muka ga wani babban jirgi a gabanmu, an rubuta sunan Saudiya baro-baro a jikinsa.''

Dayan kuma sai ya kara da cewa, ''Ana iska sosai a lokacin da muka je, mun samu mutane da yawa a cikin jirgin kuma dukkansu maza ne.''

Jirgin ya tashi sama, da kuma aka nuna daga nan kasar Masar ya nufa kamar yadda kwamfuta ta nuna, amma bayan mun tashi sama da kamar sa'a biyu da rabi sai komai ya dakata ba ma gane inda muka nufa.''

Daya daga cikin tsofaffin ma'aikatan shi ya ci gaba da bayyana cewa a lokacin da suka tashi, Yarima Sultan yana bacci, ya tashi sa'a daya gabannin saukar jirgin, ya leka ta tagar ciki sai jikinsa ya fara bari.

A lokacin da matukin jirgin ya sanar da cewa za a sauka a kasar Saudiya, sai yariman ya fara ihu da buga kofa yana kiran a zo a taimaka masa, ma'aikatan yariman sun yunkuro za su je wurinsa sai ma'aikatan jirgin suka gargade su da su zauna a inda suke.

Daya daga cikinsu ya ci gaba da cewa, ''Da muka kalli waje ta tagar jirgin, sai muka ga dandazon mutane rike da manyan bindigogi, sun kewaye jirgin cikin shirin ko-ta-kwana.''

An dauke yariman da likitansa aka kai su wani kebantaccen gida mai cike da matakan tsaro. Aka bar ma'aikatan yariman a cikin jirgin, daga bisani sai wasu mutanen na daban suka zo suka dauke su zuwa wani Otal.

Sun kwashe kwana uku ba tare da an ce musu uffan ba, babu fasfo ko wayar salula, daga bisani aka kawo musu kayansu tare da umartarsu su fice daga kasar zuwa duk inda suka so.

Daya daga cikin ma'aikatan yariman ya gane wani ma'aikacin jirgi, kuma shi ne ya ba su hakuri kan abin da ya faru ba tare da ya kara cewa komai ba.

''Abin da kawai ya shaida mana shi ne, mun zo wurin da bai dace da mu ba, a kuma baudadden lokaci, don haka yana kara ba mu hakuri kan abin da ya faru,'' in ji wani ma'aikacin Yariman.

Shi ma dayan ma'akacin ya kara da cewa, ''Ban amince da abin da ya faru gare ni ba, an sace ni, an kuma kawo ni kasar da ban sani ba, ba kuma tare da amincewata ba.''

Lamarin akwai firgitarwa, baya ga Yarima Sultan, an sace wasu mutum 18 'yan kasashen waje, kuma hukumomin Saudiyya na da hannu a sace su, don sojojin kasar ke tsare da su.

Tun daga wannan lokacin ba a kara jin duriyar Yarima Sultan ba.

Don haka an bukaci gwamnatin Saudiyya ta maida martani kan zarge-zargen da ake mata, amma har yanzu ba ta ce uffan ba.

Image caption Yarima Khaled

A bangare guda kuma, Yarima Khaled yana can kasar Jamus inda ya yi gudun hijira, amma cike da fargaba da damuwar watakila abin da ya faru ga sauran 'yan uwansa zai zo gare shi.

''Mu hudu ne 'yan uwan juna da muke zaune a kasashen Turai, muna adawa da yadda ake tafiyar da mulki a kasarmu da kuma masarautarmu, an sace uku daga cikinmu, yanzu ni kadai na yi saura,'' in ji Yarima Khaled.

Amma hakan na nufin shi ma ya na kan hanyar bacewa?

"Ina da tabbacin ba za su yi kuskuren aikata abin da suka yi wa sauran 'yan uwana ba, kuma mutane sun shaida min idan sun so yin haka ai da tuni ta faru. Sai dai ba na cikin walwala, ba na jin dadi, amma duk da hakan 'yancina yana da matukar muhimmanci.''

Labarai masu alaka