Matar shugaban kasa ta zabga wa wata waya a fuska

Dukan da matar ta ce uwargidan shugaban kasar ta mata Hakkin mallakar hoto GABRIELLA ENGELS
Image caption Dukan da matar ta ce uwargidan shugaban kasar ta mata

Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe ya zuwa yanzu ta ki bayyana gaban wata kotun Afirka ta Kudu bisa tuhumar far wa wata matashiya duk da yake jami'ai sun ce za ta je.

'Yan sandan kasar da yammacin ranar Talata sun ce ba su san inda Misis Mugabe take ba.

Wata matashiya 'yar shekara 20 ce a Afirka ta Kudu ta zargi uwargidan shugaban Zimbabwe da shauda mata wayar lantarki a ka yayin wata tashin-tashina a wani otel.

Ta kuma sanya wani hoton rauni a fuska a shafin sada zumunta. Misis Mugabe dai ba ta ce uffan ba.

Gabriella Engels ta zargi Grace Mugabe, mai shekara 52, da zabga mata waya a fuska bayan ta same ta da wasu 'ya'yanta guda biyu a wani dakin otel da ke Sandton.

Al'amarin ya faru ne da maryacen ranar Lahadi.

Tun da farko, ministan 'yan sandan Afirka ta Kudu ya ce uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe, za ta gurfana a gaban kotun game da rahotanni kan zargin cin zarafi.

Fikile Mbalula ya ce: "Ba a kama Misis Grace ba saboda ta ba da hadin kai kuma ta mika kanta ga 'yan sanda."

'Yan sandan Afirka Ta Kudu sun tabbatar cewa matashiyar ta kai rahoton far mata da nufin cutarwa.