An yi fada mafi muni a yaki da kwayoyi a Philippine

Wannan hoton da aka dauka a ranar 8 ga watan Yuli 2016, 'yan sanda ne ke binciken mutuwar wani da ake zargin mai safarar kwayoyi ne an nannade fuskarsa da wani abu a titin birnin Manila Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashe da dama sun soki lamirin gangamin da ake yi

'Yan sandan kasar Philippine sun hallaka mutum 32 a wani samame da suka kai maboyar masu safarar muggan kwayoyi, kuma wannan shi ne adadi mafi girma da aka hallaka a yakin da kasar ke yi da safarar miyagun kwayoyi.

A ranae Talata ne aka kai samamaen da aka shafe sa'a 24 ana yi a yankin Bulacan, da ke arewacin birnin Manila.

'Yan sandan sun kara da cewa wadanda aka hallaka, ana zargin masu safarar miyagun kwayoyin ne dauke da muggan makamai.

An hallaka dubban masu safarar miyagun kwayoyin, tun bayan ayyana yaki da hakan da shugaba Rodrigo Duterte ya kaddamar a 2016.

Gangamin dai an shirya yin sa da nufin kakkabe safarar miyagun kwayoyi, hakan ya ja hankalin kasashen waje da su ka yi Allah-wadai da kisan mutanen.

Samamen da aka fara da tsakar daren Talata, ya shafi yankunan Bulacan da dama kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An kuma cafke sama da mutum 100, yayin da 'yan sanda suka karbe muggan makamai da miyagun kwayoyi a yankin.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption An kama mutane da dama a samamen ciki har da manyan masu safarar kwayoyin

'Yaki da miyagun kwayoyi ka'in-da-na'in' - Howard Johnson, BBC News, Manila

Duk da cewa kasashen duniya sun yi Allah-wadai da adadin mutanen da aka hallaka, hakan ya nuna yaki da safarar miyagun kwayoyi da Shugaba Duterte ke yi ya wuce tunaninsu.

A wani taron manema labarai a birnin Manila a watan da ya wuce, cikin kakkausar murya ya gargadi masu safarar miyagun kwayoyi da cewa za su fuskanci mummunan hukuncin da sai sun gwammace kida da karatu.

A kwanakin baya na hadu da wata mace, da ta shaida min an harbe danta, a lokacin wani samame da aka kai yankin da suke.

Ta kafe kan cewa nan nata ba mai safarar miyagun kwayoyi ba ne kuma tuni ya mikawa jami'an tsaro tabar wiwi da ya ke da ita gabannin ajalinsa.

Duk da korafin da ake yi kan hallaka mutanen da wasu ke ganin ba masu safarar miyagun kwayoyi ne ba, wasu 'yan kasar na maraba da wannan mataki.

Wani direban tasi ya shaida min, an samu raguwar mutanen da ke kwace a gefen hanya.

Yayin da mazauna birnin Manila ke cewa su kam yanzu Allah-san barka don sun samu kwanciyar hankali saboda masu halin bera sun yi kaura.


Sai dai hukumomin kare hakkin bil'adam sun zargi 'yan sandan Philippine, da hallaka wadanda ba su ji ba ba su gani ba da sunan kakkabe bata gari.

Amma a nasu bangaren 'yan sandan sun nanata cewa, mutanen da aka harbe har lahira dilolin masu safarar miyagun kwayoyi ne dauke da muggan makamai.

A watan Janairu ne dai Shugaba Duterte ya dakatar da gangamin yaki da miyagun kwayoyin, tare da yin alkawarin sake daukar matakai da suka dace don ci gaba da aikin.

A kuma watan Maris ne aka dawo da gangamin da ya yi masa lakabi da ''Kawo karshen masu safarar miyagun kwayoyi, da haramta yin sa baki daya,'' lamarin da masu fafutuka ke cewa ya yi tsauri.

Labarai masu alaka

Karin bayani