Mutum 600 sun bata a Saliyo bayan zaftarewar laka

Saliyo Hakkin mallakar hoto Reuters

A kalla mutane 600 ne har yanzu ake nema bayan zaftarewar laka hade da ambaliyar ruwa da ya auku a wasu yankuna Freetown, babban birnin kasar Saliyo.

Shugaba Ernest Bai Koroma ya ayyana kwana bakwai a matsayin ranakun gudanar da alhini, da kuma bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.

An tabbatar da mutuwar kusan mutum 400, bayan zaftarewar lakar a yankin Regent da kuma ambaliyar ruwa a wasu wurare a Freetown ranar Litinin.

Hukumar agaji ta Red Cross, ta yi gargadin cewa ya kamata a hanzarta neman mutane kafin su mutu.

Kakakin fadar shugaban kasar Abdulai Baraytay, ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da tsamo gawarwaki daga cikin laka.

Duk da haka dai, ana shirin gudanar jana'izar bai daya a ranar Laraba, domin rage gawarwakin da ke dakunan ajiye gawarwaki a asibiti.

Wakilin BBC Martin Patience da ke Freetown, ya ce masu aikin agajin sun galabaita matuka saboda tsananin aikin da suke yi na ganin sun ceto jama'a.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda Bala'in zaftarewar laka da ya afkawa Saliyo

Wani jami'in hukumar agaji ta Red Cross, Abu Bakarr Tarawallie, ya ce masu aikin ceton na aiki tukuru domin ganin sun taimaka wa al'umma kafin a samu karin ambaliyar ruwa ko barkewar wata cuta.

Sakatariyar kungiyar sa ido kan ci gaban kasashen waje na Biritaniya Priti Patel, ta ce Biritaniya a shirye ta ke ta kai tallafin kayan asibiti zuwa Saliyo, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana kokarin tura masu aikin agaji.

Al'ummomin Saliyo dai har yanzu na cikin radadin wannan lamari da ya same su.

Ben Munson, na aiki ne da wata kungiyar agaji a Freetown mai suna "Street Child in Freetown," kuma ya ce ya kadu da ire-iren labaran da ya ji.

Ya ce, "Wata mata da kungiyarmu ta Street Child ta agazawa ta yi ta kuka ba tare da jin rarrashi ba, ta ji rauni a hannayenta da fuskarta, kuma duk da tana cin abincin da muka ba ta, ba ta iya cewa komai."

Ya kara da cewa, "Da ma'aikatanmu suka samu suka rarrashe ta, sai ta bayyana masu cewa an ceto ta ne daga cikin laka bayan zaftarewar kasar, amma kuma ta rasa mijinta da 'ya'yanta baki daya."

Gidajen mutanen da ke tsaunin yankin Regent sun rushe bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ranar Litinin.

Mutane da dama na ciki bacci lokacin da lamarin ya auku.

Shugaba Koroma ya yi kwalla a lokacin da ya ziyarci Regent ranar Talata, inda ya ce ibtila'in ya mamaye al'ummar kasar baki daya.

Ya ce, "An shafe al'ummar yankin baki daya, kuma dole ne mu tallafa masu yanzu."

Shugaban ya bukaci mutane su kaucewa yankunan da lamarin ya shafa.

Ambaliyar ruwa ba bakon lamari ba ne a Saliyo, inda gidajen da aka gina da laka ke cikin hatsarin rushewa sanadiyyar ruwa kamar da bakin kwarya da ake yi.

Yawanci ruwan na fadawa ne a yankunan da ke Freetown, birnin da ke da cunkoso matuka, mai mutane fiye da miliyan daya.

Labarai masu alaka