Saudiyya ta amince 'yan Qatar su yi aikin hajji

Pilgrims at the Hajj in Mecca Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An zargi Qatar da mayar da batun ibada ya zama na siyasa

Kasar Saudiyya za ta buden iyakokinta da Qatar domin maniyyata aikin Hajji su sami sauke farali, in ji kafofin watsa labarai mallakin gwamnatin kasar.

Wannan sanarwar ta biyo bayan wata ganawa ta musamman da aka yi tsakanin makwabtan kasashen tun lokacin da Saudiyyan tare da wasu kasashen Larabawa uku suka yanke huldar diflomasiyya da Qatar a watan Yuni.

Kasashen na tuhumar Qatar da tallafa wa 'yan ta'adda - abin da kasar ta sha musantawa.

Rufe iyakokin da Saudiyya ta yi ya tilastawa Qatar shiga da abinci ta teku da jirgin sama domin ciyar da mutanen kasar miliyan 2.7.

"Yan Qatar masu sha'awar sauke faralin aikin Hajjin a bana na iya shiga Saudiyya ta iyakar Salwa, in ji wani jami'in kamfanin dillancin labaran Saudiyya.

Sanarwar ta kara da cewa za a yi maraba da su idan sun isa Saudiyyar ta jiragen sama.

A watan jiya ne Saudiyya ta yi wa Qatar wani kashedi cewa maniyyatan aikin Hajji daga kasar za su fuskanci wasu tsauraran matakan tsaro idan suna son yin aikin Hajji.

Ita kuma Qatar ta mayar da martani, inda ta zargi Saudiyyan da mayar da aikin Hajjin batu na siyasa, kuma wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a yankin ya nuna rashin gamsuwarsa da matakan da Saudiyyar take son dauka.

Amma gwamnatin ta Saudiyya ta sauya ra'ayinta bayan wata ganawa da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman Al Saud ya yi da Sheikh Abdullah bin Ali bin Abdullah bin Jassim Al Thani na Qatar.

Amma masu lura da al'amuran diflomasiyya suna ganin rikicin da ke tsakanin Qatar da makwabtan nata, Saudiyya da Bahrain da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa bai kare ba.

A ranar Laraba, tashar Talabijin ta kasar Bahrain ta zargi Qatar din da kitsa makarkashiyar bata sunan gwamnatin Bahrain din a lokacin tashin hankalin shekarar 2011.


'Saudiyya ta 'dawo hayyacinta'

BBC ta tattaro martani daga yankin

Kafofin watsa labarai na Saudiyya na ta dokin bayyana wannan labarin. Wani mai sharhin al'amuran yau da kullum a tashar talabijin ta Al-Arabiya ya ce dukkan kasashen Larabawa da kasashen musulmi na "matukar murna" da wannan matakin.

Ministan harkokin kasashen waje na Hadaddiyar Daular Larabawa, Anwar Gargash ya yaba wa Saudiyyan a sakonsa na Twitter, kuma ya ce "ya kamata surutun da Qatar ke yi da kokarinta na mayar da batun aikin Hajji ya zama na siyasa ya kare bayan wannan karamci na Sarki Salman."

Amma babban editan jarida mai ra'ayin gwamnatin Qatar, Al-Arab, Abdullah al Athba, ya fada wa tashar talabijin ta Al Jazeera cewa wannan matakin na Saudiyya ya nuna "yadda ta dawo cikin hayyacinta, kuma ta daina amfani da masallatan Makkah da Madinah a matsayin makamai na siyasa kenan."

Labarai masu alaka

Karin bayani