Ana jana'izar daruruwan mutane da ambaliya ta hallaka a Saliyo

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
People are angry, reports the BBC's Martin Patience from outside Freetown's mortuary

An fara jana'izar daruruwan mutanen da suka rasu, a iftila'in zabtarewar laka a birnin Freetown na Saliyo, wanda ya faru a farkon makonnan.

Ana sa ran shugaba Ernest Bai Koroma, zai halacci jana'izar da za a yi a garin Waterloo da ke wajen birnin freetown, inda zai shiga cikin mabiya addinan Musulunci da na Kirista don nuna alhini ga wadanda suka rasu.

Ma'aikatan agaji na ci gaba da neman sama da mutum 600 da har yanzu ba a san inda suke ba tun ranar Litinin.

Mutum 3,000 ne hukumomi suka tabbatar da sun rasa muhallansu, da suke cikin tsananin bukatar taimakon matsuguni.

Dakunan ajiye gawarwaki a asibitocin da aka kai mamata sun cika makil da gawarwakin da suka fara rubewa, cikinsu akwai gawar sama da yara 100.

Sai dai an nuna damuwa matuka kan fargabar barkewar cutar amai da gudawa da zazzabin cizon sauro, kamar yadda Dakta Simeon Owizz Koroma, mai kula da cibiyar da ke sa ido don hana cututtuka yaduwa ya bayyana.

Ya kara da cewa tuni aka fara jana'izar mutanen da 'yan uwansu suka shaida da dawanda suka fatattake ba za a iya gane su ba.

An dauki gawarwakin da ba a iya tantancewa ba don yi musu jana'iza a kabari guda a garin Waterloo da aka fi sani da makabartar Ebola, wadda aka binne gawar wadanda suka mutu a lokacin barkewar cutar Ebolar a shekarar 2014 da ta hallaka sama da mutum 4,000.

Dakta Koroma ya shaidawa BBC cewa, gawarwakin da aka kawo asibitinsu sun tasamma 350, ana kuma sa ran adadin zai rubanya nan da wata guda saboda yawancin mutanen da lamarin ya shafa ginin da ya rufta ne ya binne su.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Yawancin gawawwakin da suka rube an yi jana'izarsu

Kusan baki dayan gidajen da ke yankin Regent sun ruguje, a lokacin da mamakon ruwa ya gangaro da manyan duwatsun da ke tsaunin Sugar Loaf a ranar Litinin, a lokacin da yawancin mutane ke bacci.

Iyalan mamatan da wadanda suka zo duba 'yan uwansu da ba su gani ba, sun yi cincirindo a kofar dakin ajiye gawarwakin, wasu daga ciki dauke da hotunan 'yan uwansu ko wadanda suka zo nema cike da fatan samun labarin halin da suke ciki.

Wani mutum mai suna Sorrie Koroma ya na cikin mawuyacin hali da firgici, inda ya ke fatan ganin gawar 'yarsa mai shekara 12 da ya rike hotonta a hannu, da kanwarsa da kuma wasu yara biyar da suka zo gidansa hutu, ya ce burinsa kawai ya ga gawar tasu ko hankalinsa ya kwanta.

Shugaba Koroma da ya kai ziyara yankin, ya ce an share kusan rabin al'ummar da ke zaune a yankin Regent, tare da kiran kasashen duniya su kawo musu dauki don ana cikin tsakanin bukatar taimako.

Tuni kuma aka ayyana zaman makokin kwanaki bakwai da ya fara aiki a ranar Laraba.

.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mace cikin zubda hawaye a lokacin da aka sanar da ganin gawar dan ta

Kungiyar Tarayyar Turai ta alkawarta bayar da agajin kudi euro 300,000, kamar yadda mai magana da yawun hukumar a kan al'amuran da suka shafi ayyukan agaji Carlos Martin Ruiz De Gordejuela, ya kara da cewa za su tabbatar tallafin ya kai ga wadanda suke tsananin bukatarsa.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta yi gargadin aikin ceton na tafiyar hawainiya saboda rashin kayan aiki, inda suke amfani da diga da wasu karafuna don hake baraguzan ginin.

Kasar Saliyo dai na yawan fuskantar ambaliyar ruwa, lamarin ya fi shafar wadanda ke gini a kan hanyar magudanan ruwa da idan bala'i irin wannan ya afku sun fi kowa shan wahala, yankin da sama da mutum miliyan daya ke rayuwa a wajen babban birnin kasar wato Freetown.

Labarai masu alaka

Karin bayani