Buhari ya murmure – Yakubu Dogara

Saraki da Dogara da Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Shugaba Buhari ya gana da shugabannin majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya ce Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya murmure bayan ya kwashe fiye da wata uku yana jinya a birnin Landan.

Dogara ya bayyana hakan ne bayan ya ziyarci shugaban a gidan da yake jinya a birnin Landan ranar Alhamis.

Ya ziyarci shugaban ne tare da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

"Mun ziyarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ina cikin farin ciki don na same shi cikin kyakykyawan yanayi," in ji Dogara.

Ya ci gaba da cewa: "Shugaban ya murmure sosai. Ina kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da yi masa addu'a da kuma godiya ga ubangiji don ganin shugaban ya koma gida."

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
 • 23 ga watan Yuni - Ya gana da wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar
 • 13 ga watan Agusta - Ya gana da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa

Labarai masu alaka