Cutar da ba a sani ba ta kashe mutum 62 a Nigeria

Bakuwar cuta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wacce irin cuta ce

A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan barkewar wata bakuwar cuta.

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar jihar ta fitar ta ce wadanda suka kamu da cutar suna cin ciwon mara baya ga amai da gudawa da suke yi.

Sanarwar ta ce daga farko dai an kai wadanda suka kamu da cutar asibitin koyarwar gwamnatin tarayyar kasar da ke jihar Edo, inda aka gane cewar ba zazzabin Lassa ba ne ke damunsu.

Rahotanni sun ce cutar ta fi shafar al'ummomin Fulani da ke jihar ne, wadanda yawancinsu makiyaya ne.

Tawagar lafiya ta jihar ta je yankunan da annobar ta barke, inda suka yi bincike kan ruwan sha da hanyoyin samun abincin mutanen wajen.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a duba wadanda suka kamu da cutar kyauta a asibitoci, a kuma yi gaggawar daukar matakin dakatar da yaduwarta kafin ta yi barna sosai.

Wasu rahotanni a Najeriyar na cewa hukumomi a jihar Kwara mai makwabtaka suna gudanar da bincike kan barkewar irin wannan cutar a cikin jihar.

Labarai masu alaka