China na bautar da yaran Afirka wajen tallace-tallace

Children pose for a group picture behind a black board. Hakkin mallakar hoto Featured on Taobao
Image caption Hoto guda yana kai wa dala daya zuwa hudu

Hanyoyin yin sayayya na intanet a China wato Taobao sun kawar da 'yan tallan da ake ce-ce -kuce a kansu, wadanda suke daukar bidiyo da hotunan yaran Afirka masu yin talla, hakan ya biyo bayan korafin da ake samu a game da cin zarafi.

A China masu sayen kaya suna biyan kudin talla da yaran Afirka suke yi don jayo hankalin mutane.

Alibaba wanda shi ne mai kamfanin Taobao ya ce sun dauki mataki a kan kawar da wadannan masu ciniki.

Ya shaida wa BBC cewa, "Muna sane da irin wadannan mutane da suke tallata hajarsu a shafin cinikin Taobao , kuma tuni muka dauki mataki a kan kawar da su kuma zamu ci gaba da yin haka".

Ba mu sani ba ko mahukunta za su dauki mummunan mataki a kansu, wanda ya kawo mahawara a kan batun da kuma shafikan sa da zumunta na zamani,

Tun da farko an tabbatar da Taobao na gudanar da bincike kan wasau daga cikin masu cinikin.

Hakkin mallakar hoto Featured on Taobao
Image caption Yaran sun rike alluna suna tallan kamfanoni da kayayyaki a China

Wannan hotunan yaran ne rike da allo suna cewa, "Idan kana bukatar mota bashi ka zo kamfanin Brother Long. Ka tara kudi, ka rabu da takaici. Za ku samu farin-ciki a wurinsu".

A wani allon kuma," Idan kana bukatar keke ka zo kamfanin Red Star, ku amince da mu".

Ya kuma tabbatar da cewa tallan hanya ce ta samun kudi kuma yana janyo hankalin masu sayan kaya.

Da aka tambaye shi ko kudin da ake bayarwar yana isa ga yaran sai ya ce,"Me ya sa zan damu kaina haka? Na fi damuwa da harkar kasuwancina".

Hakkin mallakar hoto Taobao
Image caption Wadansu yaran Afirka na rike da allon talla

Wasu daga cikin masu tallan Taobao sun zana wadannnan bidiyon a shafukansu, inda suke cewa yawancin kudin na tafiya a wurin yaran.

Sai dai a gaskiya yanayin yana da matukar rikitarwa fiye da yadda aketunani.

Jaridar Beijing Youth Daily ta tuntubi wani mai daukar hoton inda ya ce, abinci kadan ake ba wa yaran ko kuma a ba su kudin da ba su taka-tara ba a matsayin ladansu.

Wata mai bincike a hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar William Nee, ta bayyana yadda ake gallazawa yaran.

"A gaskiya wannnan ganganci ne, domin za a iya cin zarafin wadannan yaran. A kwai yaran da suke aiki ta hanyar rike irin wadannan hoyunan. Daga hasashen da hukumar kare hakkin dan Adam ta yi, tana iya yiyuwa daya daga cikin babban kalubalen da za a fuskanta shi ne cin zarafin yaran".

A bara ma tallan wani sabulun wanki ya jawo hargitsi da wani dan Chinar. Mai kamfanin Qiaobi ya ce bai gano cewa ba 'yan kasar ba ne har sai da ce-ce kuce ya barke.

Kuma tun shekarar 1990 ma, kamfanin man goge baki Darlie sunan wani gida ne a China, da China sunan yana nufin "man goge bakin bakar fata".

Mr Nee ya karfafa cewa, "Hakan yana nuna wasu daga cikin bambancin al'adu.......musamman idan ka zo bakar fata a Afirka".

Labarai masu alaka

Karin bayani