Lagos ne birni na biyu mai wahalar rayuwa a duniya — Rahoto

Lagos Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lagos ne birnin da ya fi ko wanne girma a Najeriya

Birnin Legas shi ne birnin da ya fi wuyar rayuwa, baya ga birnin Damascus na kasar Siriya da ke fama da yaki, in ji wani bincike na shekara-shekara.

Daya daga cikin dalilan da suka jawo hakan, in ji binciken na mujallar The Economist, shi ne barazanar da birnin Lagos ke ci gaba da fuskanta daga kungiyoyi kamar na Boko Haram, wanda hakan ke yin kafar ungulu ga samun cikakkiyar kwanciyar hankali.

Cikin watanni shiddan da suka wuce, birane 35 cikin 140 da aka bincika sun yi ta samun sauyi a matsayinsu, amma 12 daga cikinsu sun ci gaba da kasancewa a kasa, kyawun rayuwa a cikinsu na ci gaba da kasancewa kasa da kashi 50 cikin 100.

Kusan ko wnane bangare na rayuwa ba dadi.

A yayin da rahoton, wanda sashen bincike na mujallar Economist ya fitar ke nuna cewa biranen Lagos da na Damascus ne basu da saukin rayuwa, a hannu guda kuma ya ce biranen Melbourne na Australiya da Vienna na Austria ne suka fi saukin rayuwa a duniya.

Baya ga Lagos da Damascus, sauran biranen da rahoton ya ambata a matsayin wadanda ba su da saukin rayuwa sun hada da birnin Kiev na Ukraine da Douala na Kamaru da Harare na Zimbabwe da Karachi na Pakistan da Algiers na Aljeriya da Port Moresby na Papua New Guinea da Dhaka na Bangladesh da kuma Tripoli na Libiya.

Rahoton dai ya nuna cewa matakan da aka bi wajen yin binciken sun hada da yadda ake aikata miyagun laifuka, da bangaren lafiya, da yanayi, da cin hanci da kuma 'yancin fadin albarkacin baki.

An kuma fitar da bayani a rahoton kan biranen da suka fi samun ci gaba cikin shekara biyar da suka gabata, wadanda su ne Tehran da Dubai da Abidjan da Harare and Colombo; yayin da biranen da ke samun koma baya suka hada da Kiev da Damascus da Tripoli da Detroit da kuma Moscow.

Sai dai duk da cewa rahoton ya nuna yadda ayyukan ta'addanci suka sa wasu kasashen da ke Gabas ta Tsakiya da Kudancin Afirka suka zama marasa saukin rayuwa, sai dai binciken bai hada da birane irin su Kabul na Afghanistan da Bagadaza na Iraki ba.

Sai dai duk da cewa birane biyar da suka fi saukin rayuwa ba su sauya daga matakin da suke ba, an samu saye-sauye matuka cikin 'yan shekarun da suka gabata a duniya, inda guguwar ayyukan ta'addanci ta yadu a nahiyar Turai, a cewar rahoton.

Binciken dai ya yi duba ne kan birane 140.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yaki ya daidaita birnin Damascus na Syria

Labarai masu alaka