Nigeria:'Yan matan Chibok za su koma wurin iyayensu

Wasu daga cikin 'yan matan makarantar sakandaren Chibok da gwamnatin Nijeriya ta kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala dukkannin shirye-shirye na mayar da 'yan matan sakadaren Chibok da aka sako su fiye da 100 wadanda mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014 wurin iyayensu.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ministar kula da harkokin mata ta yi.

Fiye da 'yan mata 200 ne 'yan Boko Haram suka sace, amma sun sako guda 106 a cikin watannin goman da suka gabata.

Ministar matan Hajiya Aisha Jummai Alassan ta ce sai da aka kwantarwa da 'yan matan hankali tare da duba lafiyarsu, a wani shiri na maido da su cikin hayyacinsu da gyara dabi'unsu da gwamnati ta shirya, kafin mayar da su a hannun iyayensu.

Hukumomin sun ce yanzu haka duka 'yan matan su 106, sun murmure ba sa tare da wata damuwa a zukantansu, kuma sun shirya haduwa da iyayensu.

Sannan za su koma makaranta da zarar an mika su a hannun iyayensu da sauran danginsu.

Wasu daga cikin 'yan matan dai sai da aka yi musu tiyata, inda daya daga cikinsu da ta rasa kafa aka saka mata ta roba.

Ministar matan ta kuma ce za ci gaba da tattaunawa da knugiyar Boko Haram din kan sakin sauran wadanda ke hannunsu.

Batun sace 'yan mata sakandaren Chibok din dai ya ja hankalin kasashen duniya, lamarin da ya sa aka rika gangami daban-daban na jan hankalin gwamnati ta yi kokarin ceto su.

Wasu kungiyoyin kare hakkin biladama dai sun ce 'yan Boko Haram din ba wai 'yan matan Chibok kadai suka sace ba, sun sace daruruwan mata, da maza, da kananan yara.

A watan Yulin da ya gabata ne kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya, a kan ta kara kaimi wajen ganin ta kubutar da ragowar 'yan matan Chibok din da ma sauran wadanda kungiyar Boko Haram din ta sace tare da tabbatar da cewa sun koma makaranta.

Labarai masu alaka