Ra'ayi: Yaya za a magance yajin aikin malaman jami'o'i a Najeriya?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Yaya za a magance yajin aikin malaman jami'o'i a Najeriya?

A Najeriya, har yanzu kungiyar malaman jami'o'in kasar tana ci gaba da yajin aiki na sai baba ta gani da ta fara a farkon makon nan. Kungiyar dai ta tafi yajin aikin ne domin matsa wa gwamnatin kasar lamba ta biya bukatun malalan, wadanda suka hada da kara yawan kudin tafiyar da jami'o'i, da kuma kyautata walwalar malamai. Yajin aikin malaman jami'o'i dai ruwan dare ne Najeriya. Shin wane irin tasiri yajin aikin zai yi ga harkar ilimi a kasar, kuma ta yaya za a kawo karshen shi? Batun da muka tattauna a kan shi ke nan a filin na Ra'ayi Riga.