Buhari zai yi wa 'yan Nigeria jawabi ranar Litinin

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Wannan ne karo na biyu da shugaban yake tafiya jinya waje a shekarar nan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wa 'yan kasar jawabi ranar Litinin bayan ya yi fiye da wata uku yana jinya a kasar Birtaniya, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.

A ranar Asabar ne shugaban ya koma gida Najeriya.

Mai bai wa shugaban Shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya ce za a yada jawabin shugaban a kakafen yada labaran kasar ranar Litinin da misalin karfe 7:00 na safe agogon kasar.

Shugaban ya isa fadarsa a Abuja bayan saukarsa a filin jirgin sama da misalin karfe 4.36 na yammacin ranar Asabar.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne ya tafiyar da kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa yayin da shugaban yake waje.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buhari ya isa fadarsa a Abuja

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
 • 23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar
 • 26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu gwamnoni ciki har da na PDP
 • 4 ga watan Agusta- Ya gana da Archbishop na Canterbury, Justin Welby
 • 13 ga watan Agusta - Ya gana da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa
 • 18 ga watan Agusta - Ya gana da Fasto Enoch Adeboye

Labarai masu alaka