Kalli hotunan dawowar Buhari daga jinya karo na biyu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa babban birnin kasar Abuja, da misalin karfe 4.36 na yammacin ranar Asabar.

Dawowar Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Jirgin Shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Abuja da misalin karfe 4.36 na yammacin ranar Asabar daidai.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban ya sauko daga jirgi inda dumbin manya jami'an gwamnati ke dakonsa.

Bayanan hoto,

Abokin aikinmu Haruna Tangaza ya ce filin jirgin saman ya cika makil da masu tarbarsa.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Da saukowarsa ya fara gaisawa ne da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda shi ya mika wa ragamar mulkin kafin ya tafi.

Asalin hoton, Bashir Ahmed Twitter

Bayanan hoto,

Sai kuma ya dinga dagawa mutanen da ke wajen hannu yana musu jinjina alamar gaisuwa.

Asalin hoton, Bashir Ahmed Twitter

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari dai ya shafe fiye da kwana 100 yana jinya a London a karo na biyu.

Asalin hoton, Bashir Ahmed Twitter

Bayanan hoto,

Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wa Shugaba Buhari jagora inda ya dinga gaisawa da sauran mutane.

Bayanan hoto,

Rundunar tsaron fadar shugaban kasa ta yi masa faretin ban girma.