Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

'Yan hudun da aka haifa a Sokoto

Asalin hoton, SOKOTO STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Wadansu jarirai 'yan hudu - Zainab, Fatima, Ummu Khulthum da kuma Rukayyat wadanda aka yi bikin radin sunansu ranar Litinin a garin Illela na jihar Sakkwato

Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Wani mai aikin yi wa kasa hidima (NYSC) lokacin bikin kammala ba su horon mako uku a Kaduna ranar Talata

Bayanan hoto,

Wata motar jami'a da aka kama dauke da tabar wiwi a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin ranar Talata

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo lokacin da ya kai ziyara garin Minna na jihar Neja don halartar babban taro kan zuba jari ranar Litinin

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Wata mota da harin 'yan bindiga ya huda da harsashi a ofishin hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati (EFCC ) na unguwar Wuse Zone 7 a Abuja ranar Laraba

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da Shugaban Cocin Redeemed Christian Church Enoch Adeboye (daga hagu) ya ziyarce shi a birnin Landan ranar Juma'a

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya isa Abuja ranar Asabar bayan ya yi kwana 103 yana jinya a Landan