Yaushe Buhari zai kori 'kurayen' da ke gwamnatinsa?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ranar Asabar Shugaba Buhari ya koma Najeriya bayan ya yi kwana 103 a Landan

Da alama daya daga cikin manyan abubuwan da 'yan Najeriya za su so ganin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya yi shi ne ya fatattaki 'miyagun' da suke kusa da shi.

Shugaban mai shekara 74 ya koma kasar ne ranar Asabar bayan kwashe fiye da wata uku yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a Landan.

Gabanin komawarsa gida, al'amura daban-daban sun faru wadanda ake ganin da ya na nan to watakila ba za su faru ba.

Gwamnonin jihohin Kano da Zamfara sun shaida wa BBC cewa komawar shugaban kasar za ta sauya al'amura da dama.

Gwamna Abdul Aziz Yari na Zamfara ya ce "Abubuwa da yawa sun ta tasowa wadanda da a ce yana nan ba za su faru ba. Amma mu gwamnoni da mukaddashin shugaban kasa min yi bakin kokarinmu wurin magance su".

Shi kuwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce: "Wasu 'yan siyasa sun zaci ba zai dawo ba shi ya sa aka yi ta samun masu son maye gurbinsa abin da kuma ya sa aka yi ta maganganu tsakanin Kudu da Arewa".

Makiyanka, fadawanka?

Amma da alama 'yan kasar za su jira su gani ko Shugaba Buhari zai kori mutanen da mai dakinsa Aisha ta bayyana da miyagu daga kusa da shi.

A watan Yuni ne ta yi shaguben a shafinta na Facebook domin yin raddi ga wasu kalamai da dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya yi.

Abin da Sanata Shehu Sani ya wallafa:

"Tuni aka daina yi wa babban zaki addu'a, har sai ya dawo sannan za ka ga suna rawar jikin kasancewa a layin farko na 'yan kanzagi.

A yanzu kuraye da dila na ta yi wa juna rada suna kokwanton ko Sarki Zaki zai dawo ko a'a. Sarkin dai bacci yake yanzu kuma ba mai iya tabbatar da cewa zai ta shi ko ba zai tashi ba.

Amma fatan kuraye da dila shi ne kar ya tashi don su samu su zama sarakuna. A gefe guda kuwa sauran kananan dabbobi (Talakawa) na ta addu'a Sarki Zaki ya dawo don ya ceci dawa daga mugayen namun daji irin su kuraye da diloli."

Amsar da Aisha Buhari ta bayar:

"Allah ya amsa addu'ar kananan dabbobi (wato Talakawa), nan ba da dadewa ba za a fatattaki kuraye da dila daga dawa.

"Mun yi matukar yarda da addu'a da goyon bayan kananan dabbobi.

"Allah Ya ja zamanin Talakawa, Allah Ya ja zamanin Najeriya."

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kalaman nata dai sun jawo ce-ce-ku-ce da muhawara a shafukan sada zumunta a kasar.

Wasu sun jinjinawa mata, yayin da wasu kuwa ke sukarta da cewa ta aibata 'yan Najeriya da ta kira su da dabbobi marasa karfi.

Wannan dai ba shi karon farko da Aisha Buhari ke tayar da kura a kasar ba.

Ko da a shekarar 2016 a hirar da ta yi da BBC ta gargadi Shugaba Buhari da ya yi hankali da wasu makusanta wadanda ta ce su ne ke fada-a-ji a gwamnatinsa sun da yake ba su tabuka komai a yakin neman zabensa ba.

Hasalima, mai dakin shugaban kasar ta ce ba za ta yi masa yakin neman zabe ba idan ya sake tsayawa takara muddin bai kori mutanen ba sannan ya sanya 'yan jam'iyyarsa ta APC cikin mulki ba.

Kuma da alama kalaman nata sun nuna cewa batun da aka dade ana yi cewa 'yan fadi-tashi da gogayyar neman mulki a fadar gwamnatin Buharin suna hana ruwa gudu.

Sai dai wasu na yi mata kallo a matsayin macen da mijinta ya ki sakar mata linzami shi ya sa, a cewarsu, take sukar shugaban kasar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli bidiyon isowar Buhari Abuja

Labarai masu alaka