BBC ta fara yada shirye-shirye a harshen Pidgin

Pidgin

Kafar yada labarai ta BBC ta fara yada shirye-shirye da harshen Turancin Pidgin ranar Litinin don mutanen da ke yankin Afirka ta Yamma da kuma ta Tsakiya.

Harshen yana daya daga cikin manyan harshuna da ake amfani da su a wadannan yankunan.

Wannan ne karo na farko da BBC ta yi gagarumin fadada ayyukanta tun shekarun 1940.

Zuwa nan gaba kadan ne za a kara kaddamar da wasu karin sabbin harsuna 10 na Afirka da kuma nahiyar Asiya.

Kalli bidiyon farko da sashen Pidgin ta wallafa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Daga tallan biredi na koma tauraruwa gwanar kwalliya'

Kafar yada labaran mai yada shirye-shiryenta zuwa kasahen duniya tana da shirin bunkasa yadda take sayar da labaran bidiyo da kuma kafofin sada zumunta.

Pidgin wani harshe ne da ya kunshi kalmomin Turancin Inglishi da kuma wadansu kalmomi daga kananan harsuna wanda mutanen da ba sa jin yaren juna suke amfani da shi.

'Yan kasuwa ne suka fi amfani da shi a yankin Yammacin Afirka yayin cinikin bayi a gabar Tekun Atlantic a tsakankanin karni 17 da kuma 18.

Sai dai yanzu an fi amfani da shi a kasashen Najeriya da Ghana da Kamaru da kuma Equatorial Guinea.

Akwai akalla mutum miliyan 75 da suke amfani da harshen wajen tafiyar da al'amuransu na yau da kullum a Najeriya kawai.

Hakazalika ana amfani da shi a wasu kasashe da kuma yankuna na duniya.

BBC ce kafar yada labarai ta farko da za ta fara watsa shirye-shirye da harshen a Intanet da kuma kafofin sada zumunta na zamani.

Kuma za a iya samun shirye-shiryen sabon sashen a shafukan BBC Pidgin a Facebook da kuma Instagram.

Ga karin bayanin da Shugabar sabbin sassa uku da za a bude a Najeriya Bilkisu Labaran ta yi wa Nasidi Adamu Yahaya: sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Sashen Pidgin zai kasance ne a Intanet da Facebook da kuma Instagram – Bilkisu Labaran

Har ila yau, BBC za ta sake bude wasu sabbin sassa wato guda na harshen Yarabanci, da kuma na harshen Ibo.

Duka sassan uku za su rika watsa shirye-shiryensu ne daga birnin Legas a kudancin Najeriya.

Labarai masu alaka