Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Fitattun hotunan abin da ya faru a Afirka da sauran sassan duniya a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wata hazikar daliba wadda aka gayyata fadar shugaban kasar Kwaddibuwa a birnin Abidjan yayin da ta zauna a kujerarar mataimakin shugaban kasar ranar Juma'a. Yarinyar tana daya daga cikin dalibai 51 da aka girmama saboda sun ci jarabawa.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wadansu mata 'yayin da ake bikin ranar mata a kasar Tunusiya ranar Lahadin da ta gabata.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wani kabari da aka gano a kusa da kogin Nilu na kasar Masar wanda masana suka ce ya yi kimanin shekara da 2500 da hakawa.

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan tseren kasar Botswana yayin da suke kokarin mikawa juna karfe a wasan guje-guje da tsalle-tsalle na birnin Landan ranar Asabar din makon jiya.

Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar Juma'ar makon jiya, magoya bayan jam'iyya mai mulki a kasar Kenya sun fara murna bisa tsammanin cewa Shugaba Uhuru Kenyatta ne zai samu nasara a zabe. Mista Kenyatta ya doke abokin hamayyasar Raila Odinga bayan ya kaso 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Hakkin mallakar hoto AFP

Bayan kwana biyu, Mista Odinga wanda ya ki amsa shan kaye, ya yi tattaki a titunan unguwar Mathare wurin magoya bayansa suke da dama a birnin Nairobi. Sai dai daga bisani ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Hakkin mallakar hoto Roderick MaCleod/BBC

Matar wani babban jami'in hukumar zaben kasar Kenya, Chris Msando, wanda aka kashe gabanin babban zaben kasar kuma aka yi addu'o'in jana'izarsa ranar Alhamis. Marigayin shi ne yake kula da bangaren na'urorin da ke kidaya kuri'u a hukumar.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wadansu masu zanga-zanga suna daukar hoton kansu a Landan ranar Litinin, sun yi hakan ne a ci gaba da kiraye-kirayen ganin an sako dan jarida mai daukar hoto, Mahmoud Abu Zeid, wanda hukumomin Masar suka kama yayin da yake don hoton yadda sojoji suke murkushe masu zanga-zanga a sheakarar 2013.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani tela mai suna, Ganiyu Oyinlola, yayin da yake aiki a unguwar Ikeja ta jihar Legas kwanakin baya.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gabriella Engels, wata yarinya ce da take zargin Uwargidan Shugaban Zimbabwe Grace Mugabe ta ci zarafinta a kasar Afirka ta Kudu ranar Alhamis.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wadansu masu aikin hakar kabari a wajen birnin Freetown na kasar Saliyo gabanin binne mutum 400 da zabtarewar laka ya kashe ranar Litinin.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata mata wadda take neman danta bayan iftila'in zabtarewar laka a wajen wani asibiti da ke birnin Freetown.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani yaro yana kallon dakarun Majalisar Dinkin Duniya masu aikin kiyaye zaman lafiya a sansanin 'yan gudun hijiran Al-Nimir a kasar Sudan, wanda yake dauke da 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu fiye da dubu biyar. Galibin masu tserewa rikicin Sudan ta Kudu suna guduwa kasar Uganda ne wacce ta karbi 'yan gudun hijiran Sudan ta Kudu kimanin miliyan daya.

Labarai masu alaka