Me mutane ke cewa kan jawabin Shugaba Buhari?

Kafofin sada zumunta Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar Najeriya jawabi a safiyar ranar Litinin, jama'a a kasar suka fara bayyana ra'ayoyinsu musamman a kafofin sada zumunta a kasar.

Jama'a sun rika tsokaci game da jawabin mai tsawon minti 4.40 inda wasu suke korafi game da yadda shugaban bai yi karin haske ba game da halin lafiyarsa.

A muhawarar da aka tafka a shafukan sada zumunta na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu.

Ga kadan daga cikinsu:

Shuaibu Adam Bagwai cewa ya yi:

"Shugaba Buhari bai kamata ma ka yi magana a kan wadancan wawayen mutanen ba, amma hakan ma babu komi tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro."

Shi kuwa Dan Asabe Soro nuna farin cikinsa ya yi da jin muryar shugaban.

"Cuta ba mutuwa Allah mai iko a kan komai ga shi ya dawo gida toh masu fafutukar ballewa daga Nigeria sai ku shirya domin fa Nigeria kasa daya ce kuma haka muka santa babu wanda zai zo ya kawo mana rudani face Allah ya yi mana maganinsa. Dattijo Allah Ya kara lafiy,"in ji shi.

Na dawo bakin aikina — Buhari

Zan yaki 'yan ta'adda da miyagu – Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Babu wanda ya isa ya raba Najeriya – Buhari

"Alhamdulillah, Alhamdulillahi, yau take ranar farin ciki a kasata Najeriya Baba Buhari ni na ma rasa wani irin murna da jin dadi zan nuna ma in kasata Najeriya a yau ranar Litinin," in ji Sabitu Ibn Saliss.

Akwai kuma ra'ayin da ya dace shugaban ya yi garanbawul a majalisar ministocinsa, kamar yadda Sani A. Sani ya ce:

"Shugaba Buhari mun ji dadin jawabinka sosai. Abin da ya rage mu ji ka yi garanbawul a majalisar ministocinka. Tun lokacin da ka tafi neman lafiya babu abin da suka yi," kamar yadda ya bayyana.

Amma Abubakar Baban Rabi Sarina ya bukaci shugaban ya warware matsalolin kasar:

"To Buhari ya kamata ku yi kokarin magance mana matsalolin da suka addabi kasarmu Najeriya."

Baya ga shafukan sada zumuntar BBC Hausa, wasu mutanen da dama suna tsokacin ne a shafukansu na kashin kansu.

Akwai Rahama Abdulmajid da ke cewa, ga alama dai jawabin shugaban ya nuna gyara za a ci gaba da yi ba aiki ba tukunna. Hakan ya jawo muhawara sosai a shafin nata.

"Ina ma a ce Baba Buhari zai dauki niyyar sassautawa talakawa, ya bude boda, ya sassauta farashin dala, ya rage kudin man fetur da na lantarki. Kawai Saboda ya saukakawa talakawan da suke ta addu'a Allah ya ba shi lafiya, Allah ya tausaya masa.Shi ma sai ya tausaya mana." Sheriff Almuhajir kenan wani ma'abocin amfani da shafukan sada zumunta, a nasa rubutun a shafin Faceebook.

Labarai masu alaka