Rashin bandaki ya kashe aure a Indiya

Allon da ke nuna alamun akwai bandaki na mata da maza Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yin bahaya a waje ba bakon abu ba ne a sassa da dama na Indiya

An bai wa wata mata 'yar kasar Indiya damar rabuwa da mijinta saboda ya ki gida bandaki a gidansa.

Matar mai shekara 20 ta kwashe shekara biyar da yin aure, amma a tsawon wannan lokacin dole ta fita sararin Allah ta yi ba haya da sauran bukatunta.

Dokar indiya ta amince a yi saki a wasu takaitattun yanayi kamar cin zarafi a cikin gida ga kuma mugunta idan har an tabbatar da hakan.

Lauyan da ke kare matar ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, alkalin ya ce tilasta mata yin bahaya a waje wani nau'i ne na azaftarwa.

Kotun wadda ke zamanta a jihar Rajasthan ta ce a mafiya yawan lokuta ana tilastawa mata jira har sai duhu ya yi kafin su fita sarariin Allah su biya bukatunsu, saboda babu bandakuna a gidajensu.

Jaridar Times of India ta ambato alkalin kotun yana cewa: " Muna kashe kudi wajen sayen taba sigari da barasa da wayoyin salula, amma ba ma son gina bandakuna domin kare mutuncin iyalinmu.

"A kauyuka da dama dole mata su jira har sai rana ta fadi kafin su je daji su yi bahaya. Wannan ba mugunta ba ce kadai har ma da keta mutuncin mata. "

Jaridar ta ce matar dai ta shigar da karar ce a shekarar 2015 inda ta nemi kotun ta kashe aurenta.

Yin fitsari da bahaya a waje wani abu ne ruwan dare a sassa da dama na yankunan karkara a kasar Indiya. Gwamnati ta bullo da wani shiri na gina bandakuna a kowane gida a yankunan karkara nan da shekarar 2019, amma shirin na fuskatar turjiya.

Haka kuma gwamnatin ta zuba kudi a shirin ne saboda rashin kyautata wa mata saboda tilasta musu yin doguwar tafiya zuwa wani wuri domin biyan bukatunsu a cikin dare.

Bugu da kari kuma inda ma aka gina bandakunan ba a amfani da su duk kuwa da cututtukan da ake dauka wanda ake alakantawa da bahaya.

A bara asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya yi kiyasin cewa rabin al'umar Indiya basa amfani da bandaki.

Labarai masu alaka

Karin bayani