Mutane na kallon kisfewar rana
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda rana ta yi husufi dundum a Amurka

Kalli yadda rana ta kisfe a Amurka, daga wani gabar teku zuwa wani, wanda rabon da a yi kisfewar rana dumdum irin wannan tun shekarar 1918, lokacin da aka yi a dukkan kasar Amurka, daga jihar Oregon a yammaci zuwa jihar South Carloina a gabashi.

Mutane a Amurka suna shirye-shiryen ganin kisferwar rana mai ban mamaki.

A yayin da wata ya bi ta gaban rana, inuwar watan za ta bayyana wacce za ta ratsa Amurka, daga gabar tekun Pacific zuwa gabar tekun Atlantika.

Za a ga inuwar watan baka kirin a fadin nisan kilomita 113, amma kuma wasu sassan da suke kusa da wannan yankin ba za su ga cikakken husufin ba, sai dai wani sashe na inuwar watan.

Bayanai: Reuters Live/NASA TV