'Jawabin Buhari bai isa ya yaudare mu ba'

President Buhari giving his televised address Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari ya shafe fiye da wata biyar yana jinya a Burtaniya a bana.

Wani jagoran masu fafutukar kafa Biafra daga Nijeriya ya ce kasar ta wuce matakin ci gaba da kasancewa a matsayin Nijeriya kasa guda.

Comrade Uchenna Madu na kungiyar Massob ya fada yayin zantawa da BBC don mayar da martani ga jawabin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, cewa wajibi ne a tattauna matsalar zamantakewar Nijeriya.

Shi dai, Muhammadu Buhari yayin jawabinsa a safiyar ranar Litinin bayan ya koma kasar daga jinyar fiye da kwana 100 a London, ya ce zaman Nijeriya dunkulalliyar kasa, batu ne da bakin alkalami ya riga ya bushe.

Sai dai Kwamared Uchenna Madu ya ce ba a isa a yaudare su ba. Kuma jawabin shugaban kasar na ɓad-da-bami ba za a iya yaudararsu ba.

"Abin da duk (Buhari) ya fada, mu a wajenmu shirme ne kawai", in ji shi.

Ya ce jawabin shugaban kasar ya gaza, wajen tabo ainihin tushen matsalar da ta shafi batun hadin kai da dunkulewar kasar wajen guda.

A cewarsa: "Ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba, kan gwagwarmayar tabbatarwa da dawo da kasar Biafra. Kuma ba za a taba karya mana gwiwa ba, don haka za mu ci gaba da matsin lamba bisa tsarin da muke bi ba tare da tashin hankali ba."

Uchenna Madu ya ce tafiyar tabbatar da kasar Biafra ta kai zangon da ba a komawa. "Babu ta yadda za a yi a koma baya."

"Saboda mun tsallake iyaka da matakin ci gaba da kasancewa a matsayin Nijeriya kasa guda."