Kun san alkhairan da ke cikin kwanaki 10 na watan Zul-Hajji?

Miliyoyin musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke gudanar da aikin Hajji a duk shekara
Image caption Aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci 5

Watan Zhul Hijjah shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci, kuma a cikinsa ne ake gudanar da aikin hajji wanda yana cikin shika-shikan musulunci guda biyar da ake so ko wanne musulmi ya yi idan ya samu iko.

Daga cikin falalar kwanaki goma na farkon wannan wata, malamai sun ce an samu Hadisi daga Manzon Allah SAW da yake cewa: "Babu wani aiki a wajen ALlah SWT da yake da matukar lada kamar aikin da bawa zai yi a kwanakin 10 na farkon Zul Hijja. Sai Sahabbai suka tambaye shi, 'Ko da kuwa jihadi ne saboda Allah?' Manzo SAW ya amsa da cewa, "Ko da kuwa jihadi ne saboda, sai dai idan mutum ya fita jihadin da dukkan dukiyarsa ya kuma koma gida ba tare da komai ba." Bukhari ne ya ruwaito.

Malama da dama sun ce kamar yadda kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ke da falala, haka ma kwanaki 10 na farkon Zul Hijjah ke da falala.

Daga cikin falalarsu kuwa akwai ayyukan da ake so bawa ya dukufa yi na ibada don neman yardar Allah.

1. Daga cikin falalar kwanaki 10 na farkon watan Zul Hijjah akwai yin aikin Hajji'

Aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda 5, da Allah SWA ya umarci dukkan musulmai gudanar da shi akalla sau daya a rayuwarsa.

Aikin Hajji ya wajaba akan wanda ya ke da lafiyar jiki, da lafiyar yin tafiyar, da kuma abin da zai yi guzuri da shi, tun daga yin tafiya zuwa kasa mai tsarki (makka) daga duk inda ya ke a duniya.

2. Ana so mutum ya yi azumi a kwanaki taran farko na watan, musamman ma na ranar Arafah.

Malamai Hussaini Zakariyya ya ce azumin Arfah yana da falala sosai amma ba farilla ba ne, amma Ubangiji ya yi alkawarin gafartawa wanda ya azumci yinin.

3. Ana so a yawaita zikiri da kabbara a wadannan ranaku 10 na farkon watan Zul Hijjah.

4. A yawaita yin sallar dare

5. Ana so bawa ya yawaita tuba da neman gafarar Ubangijinsa.

6. Ana so mutum ya yawaita karatun Al-qur'ani.

7. Ana so mutum ya kara kaimi wajen yin kyawawan ayyuka kamar sadaka da taimako da sauransu.

8. Yin layya a ranar goma ga watan Zul Hijjah ga wanda yake da halin abin yankawa.

9. Halartar sallar Idi.

10. Yawaita yin godiya ga Allah Subhanahu wa ta'ala.

Kaza lika akwai batun da ke cewa bai halatta mutum ya yanke farce ko yin aski ko ga mace gashinta ya zuba ba idan har akwai niyyar yin layya.

Sai dai Ustaz Hussain Zakariyya ya ce ba haka abin yake ba, wancan hukuncin ya hau kan wadanda suka tafi aikin hajji ne kawai ban da wadanda ba su samu zuwa ba.

Ga dai Sheikh Hussain Zakariya da karin bayani, kan abubuwan da ya kamata musulmi su yi a kwanaki 10 na farkon watan Hajji, ko da kuwa ba su samu damar zuwa kasa mai tsarki ba:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Sheikh Hussaini Zakariyya kan falalar Zhul Hijjah

Labarai masu alaka