Saudi Arabia: An kama yaron da ya yi rawar 'Macarena'

Three collaged screengrabs show a teen wearing a stripey shirt and sport shorts at various stages of doing the popular Macarena dance in a Saudi street Hakkin mallakar hoto TWITTER @ahmed
Image caption Dubban mutane sun kalli bidiyon kuma sun tura wa abokansu domin su ma su gani

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama wani yaro mai shekara 14 wanda aka nuna a wani bidiyo yana taka rawar wakar 'Macarena' a kan titi.

Bidiyon ya ja hankulan dubban mutane a Twitter.

Hukumomi na yi wa yaron tambayoyi bayan an zarge shi da "nuna rashin tarbiyya" a birnin Jeddah, in ji wata sanarwa.

Ba a tabbatar da ko yaron dan kasar ta Saudiyya ne ba, kuma ko hukuma za ta gurfanar da shi a kotu.

A farkon wannan watan aka kama wani mawaki a kasar saboda ya yi rawar "dab" a yayin da yake waka a yankin kudu maso yammacin kasar,

A cikin bidiyon mai tsawon dakika 45, an ga yaron yana hana motoci wucewa a yayin da yake taka rawar wakar ta Macarena wadda ta yi tashe a shekarun 1990.

Ana ganin an saka bidiyon ne tun a watan Yulin bara.

Saboda rashin rubutacciyar doka a Saudiyya, jami'ai da alkalai na da iko mai yawa wajen hukunta yara kanana a kasar mai bin tsattsauran ra'ayin addini.

Bidiyon ya raba hankulan masu ziyartar shafukan sada zumunta, inda wasu ke kare yaron, har suna kiransa "gwarzo".

Wasu kuma sun soki halayyarsa, suna kiran abin da ya yi "rashin tarbiyya".

Labarai masu alaka

Karin bayani