'Dokar hana saki uku a Nigeria ba mafita ba ce'

Wedding hands Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani Malamin addinin musulunci a Abuja, babban birnin Nijeriya ya ce kafa doka don haramta saki uku take-yanke ga matan aure ba hanya ce mai bullewa ba a kasar.

Ustaz Usaini Zakariyya ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da BBC kan dakatar da al'adar yin saki uku tashi daya da Kotun Kolin Indiya ta yi a kasar ranar Talata.

Ya ce hukuma ba za ta iya hana saki, sai idan mutane sun samu ilmi ta yadda za su san cewa aure amana ce kuma dole a kiyaye ta idan ana son tsira a anar kiyama

"Duk bangare biyu (a zamantakewar aure) na da 'yancin neman rabuwa da juna, don haka ba miji ne kadai yake da ikon saki ba, in ji Sheikh Zakariyya.

Malamin ya ce ba a son yin saki fiye da sau daya a lokaci guda don kuwa a cewarsa: "Saki uku gaba daya wasa da aure ne kuma wasa da shari'ah ne."

Sheikh Usaini Zakariyya ya ce ko da yake, Allah ya ba mutum damar "ka saki matarka, amma bai amince da sakin wulakanci irin wannan ba".

Ya ce rashin tsoron Allah kan sa mutum ya karya dokar da Allah ya shimfida masa, yayin da jahilci ke sanya karya dokokin da aka yi don kyautata rayuwarsa.

A cewarsa kafa dokar a Nijeriya kamar yadda Indiya ke kokarin yi, ba mafita ba ce ga hana yin saki barkatai a kasar.

Don haka ya nanata wajibcin ilmantar da mata kafin aure ta yadda za ta san hakkokinta da kuma hakkokin mijinta a kanta.