Buhari ya soke taron ministocin na wannan makon

Ana yin taron majalisar ministoci da shugaban kasa ne a duk ranar Laraba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yin taron majalisar ministoci da shugaban kasa ne a duk ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke taron ministoci na wannan mako, wanda shi ne na farko da aka yi tsammanin zai halarta bayan dawowarsa daga jinyar da ya shafe fiye da wata uku yana yi a Birtaniya.

Mai ba shi shawara ba musamman kan harkar yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba da safe gabannin lokacin da aka saba fara taron.

Ba a dai bayyana dalilin daukar wanan mataki ba, amma dama shugaban yana aiki ne daga gida tun bayan dawowarsa daga jinya a ranar Asabar.

Mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ne ya ce Shugaba Buharin zai dinga aiki daga gida ne saboda ana gyaran ofishinsa wanda beraye da kwari suka lalata a lokacin da ba ya nan.

Sai dai a sanarwar, Mr Adesina ya ce, Shugaba Buharin zai karbi rahoto ne daga kwamitin da aka dorawa alhakin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa wasu jami'an gwamnati biyu, Shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasa, Chief Ayo Oke, da Sakataren gwamnati Babachir Lawal, wadanda tuni aka dakatar da su.

Mataimakin shugaba Buhari Yemi Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban a lokacin da ba ya nan, ne yake shugabantar kwamitin.

A yayin da Shugaba Buhari yake jinyar dai 'yan Najeriya da dama sun yi ta kiransa da ya sauka daga mulkin, a ganinsu ba shi da lafiyar da zai iya jagorantar kasar.

Sai dai shugaban bai taba cewa ga irin ciewon das ke damunsa ba.

Ko a wancan karon ma da shugaban ya dawo daga jinya bai taba halartar taron ministocin na mako-mako ba har zuwa lokacin da ya sake komawa Birtaniya jinya a karo na biyu.

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Shugaba Buhari zai karbi rahoton ne daga hannun mataimakinsa Osinbajo

Labarai masu alaka