'Yadda 'ya'yana 14 suka mutu a zaftarewar laka'

Alfred Johnny talks to friend beside the broken house and mudslide Hakkin mallakar hoto Olivia Acland

Fiye da mutum 3,000 ne suka rasa muhallansu a bala'in zaftarewar laka da ya faru a Saliyo a makon da ya gabata, wanda ya hallaka akalla mutum 499, inda har yanzu ba a gano inda mutum 600 suka shiga ba.

Wani mai aikin sa-kai Fessellie Marah, ya ce: "Zai yi wahala a san ainihin yawan mutanen da abin ya shafa, saboda wasu gawawwakin ma sun zagwanye. Har yanzu muna zakulo bangarorin jikin mutane a karkashin baraguzai.

Wani bangare na tsaunin Sugar Loaf ne ya rufta kan wata unguwa da ake kira Regent da misalin karfe 05:45 na asubahin ranar Litinin. Hakan ya sa ruwa da laka da duwatsu suka dinga kwararowa daga saman tsaunin, inda suka yi ta rushe gidaje a wasu yankuna biyu daban Kamayama and Kaningo.

'Yar jarida Olivia Acland ta tattauna da wasu da suka tsira.


'Na kidime ina kallon tsauni na ruftawa'

Daga kasan tsaunin a yankin Regent, wani gida da bai gama rushewa ba, ya tsaya a tsakanin sama da kasa.

Wani magidanci Alfred Johnny, na kara-kaina a tsakanin baraguzai yana shan taba kuma yana ta yin waya. Ya rasa abokai uku, wadanda dukkansu suna cikin gidan a lokacin da tsaunin ya rufto.

Alfred eside the broken house and mudslide Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Alfred Johnny yana kula ne da gidan wanda ya zama mallakin 'yan uwansa biyu da suke zama a kasar Australiya

Ya ce: "Ina zaune ne a karamin gidan da yake baya, " ya fada yana nuna wani dan karamin gida da ya lalace amma bai rushe ba.

"Babban gidan na Yayana ne. Yana zaune a Australiya. Ni ne nake kula da gidan. Wasu ma'aikata biyu da wani injiniya na zaune a ciki.

"Ina tsaye a baranda lokacin da zaftarewar lakar ta afku. Na ji wata kara mai karfi sosai, kamar ana fasa nakiya. Sai duwatsu suka fara zubowa kasa. Daya ya fado kusa da ni har na fadi. Jikina ya hau bari kamar ana kada min gangi.

"Na yi kokarin guduwa na kuma bude kofar gidan ta gaba amma sai duwatsun suka ci gaba da zubowa. Ba zai yiwu na matsa ko nan da can ba.

"Na kidime kawai ina kallon yadda tsaunin nan ke ruftowa. Manyan duwatsu na fadowa gefen gidaje. Ta ko ina mutane sai ihu suke. Ina kallo har sai da ko wanne gida ya rushe," in ji Mr Johnny.

Ya tafi ya nuna min wajen da ya tsaya yana kallo yayin da rediyonsa, daya daga cikin abubuwa kadan da suka rage masa a gidansa da ya yi ambaliya, ta fara wata waka. Wakar ita ce "Oh Allah ka ceci Saliyo, oh Allah ka taimaki Saliyo, ke ceci wannan kasar da muke so."

Mr Johnny ya yi kokarin kwashee laka da ruwa daga daki daya na cikin gidansa, kuma a nan yake zaune har yanzu. Katifarsa ta lalace don haka kwalaye ya shimfida a kan gadonsa. Kayayyakinsa da laka ta bata kuma ya jibge su a wani dakin daban, inda nan ma laka ta taru a kasa sosai.


'Ina ganin barnar na san cewa na rasa 'ya'yana'

Daga sama kadan hanyar hawa tsaunin akwai wani mutum da wata mata suna zaune kan tarin duwatsu. Dukkansu sun yi shiru, suna kallon nesa.

Matar, Yatta Kamara, ta ce: "Na rasa mutum 14 a gidana. Na bar gida a wannan yammacin don na karbo shinkafa daga gidan wata Innata saboda ba mu da abin da za mu ci, kuma ina bukatar ciyar da 'ya'yana.

Yatta Kamara and her brother Mohammed Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Yatta da dan uwanta na zaune suna jimamin rashe-rashen da suka yi

"A lokacin da na isa gidan Innata, an fara sheka ruwa kamar da bakin kwarya don haka ta ce min na kwana da safe sai na koma gida.

"Da gari ya waye da misalin karfe 06:30 na safe ina wanka, don shirin tafiya gida, sai ga wani makwabcinmu da gudu yana cewa: 'Tsauni ya rufto, ya kuma binne gidanki da duk 'ya'yanki.'

"Na fita a guje zuwa gida sai na ga dumbin jama'a kuma laka ta binne dukkan yankin. Ina ganin wanan barnar na san cewa lallai na yi rashi," in ji Ms Kamara.

Ta ce min na jira minti daya, sai ta garzaya ta samo min hoton wadanda suka mutu, ciki har da 'ya'yanta hudu da jikanta jariri.

Photograph of Yatta's two dead children and dead grandchild Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Yatta ta arsa 'ya'yanta hudu da jikanta

"Wannan ce karamar 'yata, Jeneba," ta fada tana nuna wata yarinya 'yar shekara shida da take tsaye rike da jariri a hannunta.

A yanzu haka Ms Kamara na zaune ne da dan'uwanta Mohammed, wanda ke zaune a wani yanki can gabas da birnin Freetown. Ta koma Regent ne don ta karbi kayan abinci daga wata kungiyar agaji ta Street Child.

Ta kura ido a karo na biyu ta ce: "Na rasa komai."


'Ta rufin kwano na tsira'

A al'ummar Kaningo, wadda ke kasa da kogi, Abdul Mansaray yana kokarin kwashe laka daga cikin gidansa.

Abdul Mansaray claning his house Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Abdul Mansaray da iyalansa sun samu sun tsira ne ta saman rufi

Tare da dan uwansa da abokansa biyu, yana kwashe lakar da shebur yana kai wa waje. Akwai alamar inda ruwa ya ratsa ya shiga. Yana tsaye a gaban dakin daidai inda rufin kwanon ya yaye.

Ya ce: "Ta wannan ramin muka tsere. Ruwa ne ya cika dakina a lokacin da na farka, don haka na tafi na tashi matata da 'ya'yana da dan'uwana."

"Mun yi kokarin barin gidan ta ainihin kofa sai dai a lokacin ruwan ya karu, har ya kawo gwiwata. Ba mu iya bude kofar gaban ba saboda akwai ruwa ta kowanne bangare.

"Sai muka bi ta kofar baya ita ma muka kasa bude ta. Sai na dudduba na hango tabarya.

"Na balla rufin kwanon da tabaryar da taimakon dan'uwana, na yi kokarin hawa kan rufin. Daga saman rufin ina kallon yadda kayan jama'a ke gudu a saman ruwa.

"Na hango tsani yana gudu a kan ruwa, sai na sauka na dauko shi. Na tura shi cikin kofar dakin nan don matata da 'ya'yana da dan'uwana su kama su hauro.

"Mun tsaya a barandar makwabcina muna kallon yadda ruwan ke karuwa. Mun gode Allah da ya sa muka tsira, duk da cewa dai na rasa dukkan dukiyata."

Abdul Mansaray sitting on the ladder that saved him and his family Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Abdul Mansaray na zaune kan kurangar da ya ceto iyalansa da ita

Mr Mansaray na daya daga cikin dubban mutanen da suka rasa dukkan abin da suka mallaka har da gidansa.

Kamar yadda makwabcinsa ya ce: "Kadan daga cikin al'ummar Saliyo ne ke ajiye kudi a banki, yawanci ma yin hakan sai ma'aikata. Amma sauran mutane duk a gida suke ajiye kudinsu."

Matarsa da 'ya'yansa sun koma kauye da ke kudancin kasar, amma Mr Mansaray da dan uwansa suna zaune da wani makwabcinsu wanda ke zaune a can saman dutse a yankin.

"Muna kokarin gyara gidan ne ta yadda iyalaina za su iya dawowa," in ji Mr Mansaray.

Na tambaye shi game da hadarin zama a wajen, da kuma yiwuwar saken samun wata zaftarewar lakar ko ambaliya. Sai ya amsa da cewa: "To ina nake da shi da zan iya zuwa?"


'Yaya iyayena za su biya kudin makarantata?'

Mbalu Bangura na zaune a wannan yanki. Shekararta 15, kuma damuwarta ita ce ba za ta iya komawa makaranta ba.

Mbalu Bangura at Kaningo school collecting emergency supplies Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Mbalu ta kubutar da kanta da sauran kannenta hudu

"Ta yaya iyayena za su biya min kudin makaranta?" a cewarta. "Mun rasa komai a gidan nan, littattafaina da kayan makarantata da dukkan dukiyarmu."

Tana dingishi sosai kuma an sanya mata bandeji a kafarta. Ta ce kwalba ce ta fashe mata a kafa lokacin da take gudun ceton rai.

"Muna neman tsira ta wata fasasshiyar taga saboda dukkan kofofin gidan sun ki buduwa," in ji ta.

"Ina da kanne hudu kanana kuma duk ni na mika su ta taga ga iyayensa. Ruwan yana shigowa da gudu har kusan kirjina.

"Mun tsallaka ta ruwan dauke da kananan yaran. Amma dai duk mun tsira. Sai kwalba ta fado kan kafata a lokacin da muke gudu. Wani mai aikin agaji ne ya kai ni asibiti," in ji Ms Bangura.


'Wani katon dutse ne ya turmushe su duka'

Kadiatu Bendu na zaune ne a Kamayama Pentagon, wata unguwa mai nisan mil biyu daga wajen da abin ya faru. Tana jiran taimako da kungiyoyin agaji.

Kadiatu Bendu and Edna collecting emergency supplies Hakkin mallakar hoto Olivia Acland
Image caption Kadiatu na kallo mijinta da 'yarta suka mutu

A yanzu tana zaune ne da wani dan uwanta, wanda yake da wani karamin gida mai daki uku. Baya ga Kadiatu da 'yarta, ya bai wa wasu mutum takwas din muhalli a cikin gidansa, hakan na nufin a yanzu mutum 17 ke zaune a dan karamin gidan nasa.

"Abin ba sauki ko kadan - muna da yawa a gidan nasa," in ji Mrs Bendu.

Duk da cewa ta tserar da 'yarta Edna mai wata hudu a duniya wacce ta makale ta gam a kafadarta, amma ta rasa mijinta da 'yarta mai shekara 16.

"Mijina ne ya tashe ni a lokacin da ruwa ya fara cikia mana gidan. A lokacin tuni rufin kwanon gidan ya rufto saboda matsanancin ruwan sama da ake yi. Ya taimaka min na hau saman rufin ni da Edna wacce na goyata a bayana, sai ya koma don ya taso daya 'yar tamu.

"Yana taimakonta don ta hau saman rufin ne sai wani katon dutse ya rufto cikin gidan daga daya bangaren ya murkushe su. Ina ganin lokacin da hakan ta faru. Rufin dakin dai bai rufto ba don na kakkarfan katako ne, " in ji Bendu.

Dukkan hotunan an same su ne daga: Olivia Acland

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC