Angola na zaben sabon shugaba bayan shekara 38

Supporters of Angola's Casa-CE party Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Matasa na cewa babban burinsu a samar musu da ayyukan yi

A ranar Laraba ne 'yan kasar Angola ke zabe sabon shugaba.

Jose Eduardo dos Santos ya hau kan mulkin kasar mai arzikin man fetur tun shekarar 1979, inda ya zama shugaba na biyu da ya fi kowa dadewa a mulki a duniya.

Bai tsaya takara a wannan zaben ba - Ministan Tsaron kasar Joao Lourenco ne ya tsaya karkashin jam'iyya mai mulki ta MPLA.

Babban abokin hamayyarsa shi ne Isias Samakuva, na jam'iyyar adawa ta Unita tsawon shekara 27 da aka yi ana yakin basasa.

Karkashin tsarin zaben Angola, mutane na zabar dan takara ne da kuma jam'iyya a zabe guda.

Image caption MAsu kada kuri'a suna da zabin zabar 'yan takara shida da jam'iyyu daban-daban

Masu sharhi na cewa jam'iyyar MPLA wacce take kan mulki tun samun 'yancin kan kasar daga Portugal a shekarar 1975, ce za ta lashe zaben.

A zaben da aka gudanar a baya, jam'iyyar Casa-CE alliance ce ta samu kashi uku na yawancin kujeru. Abel Chivukuvuku ne jagoranta wanda ya balle daga jam'iyyar Unita.

A rumfunan zabe: Daga wakilin BBC a Luanda, Clare Spencer

Masu kada kuri'a sun kafa layi don jiran su fara kada kuri'a tun da safiyar Laraba a Luanda babban birnin Angola.

An fara barin tsofaffi su fara kada kuri'a don zaben wanda zai maye gurbin Shugaba Jose Eduardo dos Santos.

Akwai alamar kwanciyar hankali a birnin, kuma an bayar da hutun aiki saboda mutane su samu damar kada kuri'a.

Jam'iyyar adawa ta Unita ta samu kashi 18 cikin 100 na kuri'u a wancan zaben da aka gudanar. Masu sharhi za su sa ido sosai don ganin ko jam'iyyar adawa za ta samu damar kara yawan kuri'unta a wannan karon.

Jam'iyyar adawa ta Casa-CE ta ce an kama fiye da mutum 20 na masu sa idonta a daren Talata a Launda saboda sun yi zanga-zanga.

Sun nemi cewa sai an ba su damar sa ido kan yadda kada kuri'un zai kasance, amma an hana su damar.

Gwamnati ta hana zanga-zanga a lokacin yakin neman zabe, amma ranar Litinin ce rana ta karshe ta yakin neman zabe.

Ba a dai sani ba ko har yanzu suna hannun hukuma kuma ba a san ainihin tuhumar da ake musu ba.

Wakilin BBC Mayeni Jones da ke Luanda ya ce matasan kasar na da muhimman abubuwan da suke so daban da na manyansu, a yayin da suke kada kuri'unsu.

A baya dai babban burin 'yan kasar shi ne zaman lafiya, sakamakon yakin basasar da aka yi wanda aka gama shi a shekarar 2002.

Amma matasa suna shaida wa BBC cewa babban abin da suka fi so shi ne - a samar musu da ayyukan yi.

Masu sukar lamirin gwamnati na cewa cin hanci a kasar na nufin wadakar da masu mulki ke yi da arzikin man fetur.

Hakkin mallakar hoto AFP

Bayan gama yakin basasar, Angola na daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa a duniya saboda kudin shigar da take samu daga man fetur.

Amma bayan da farashin man fetur ya fadi a kasuwar duniya a shekarar da ta gabata, hakan ya shafi tattalin arzikinta.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kun san shugaban kasar da ya shekara 38 a mulki?

Duk da cewa Mr Dos Santos zai sauka daga mulkin kasar, amma shi ne zai ci gaba da kasancewa shugaban jam'iyyar MPLA, yayin da 'ya'yansa kuma suke rike da manyan mukaman gwamnati.

Labarai masu alaka

Karin bayani