Wanne mataki Buhari zai dauka kan Babachir?

Buhari da Osinbajo Hakkin mallakar hoto Office of Vice President
Image caption Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya mikawa Shugaba Buhari rahoton

Hankulan wasu 'yan Najeriya sun karkata zuwa irin matakin da shugaban Najeriya zai dauka kan sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaban hukumar leken asirin Najeriya da aka dakatar kan zarginsu da aikata ba-dai-dai-ba.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya dai ya karbi sakamakon binciken da aka gudanar kan zargin almundahana da ake yi wa manyan jami'an gwamnatinnasa biyu ne a ranar Laraba.

A watan Afrilu ne dai shugaban ya umarci wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakinsa ya binciki sakataren gwamnatin kasar da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, bayan dakatar dasu bisa zarge-zarge daban-daban na almundahana.

Sai dai a bangare guda fadar shugaban ta sanar da dage zaman majalisar ministoci da ya kamata ya shugabanta a yau a karon farko cikin watanni da dama.

Tun a ranar 8 ga watan Mayu ne aka shirya shugaban kasar zai karbi rahoton amma sai rashin lafiyarsa ta hana hakan, inda ya koma Landan don ganin likita ranar 7 ga watan Mayu.

Ga dai karin bayani daga abokin aikinmu Haruna Shehu Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Haruna Tangaza kan rahoton Babachir
Hakkin mallakar hoto Office of Vice President