An soki manhajar fallasa asirin 'ya'ya masu luwaɗi

Internet User Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanoni da dama ne a yanzu suke sayar da na'urorin bibiyar yadda 'ya'ya suke amfani da intanet

An soki lamirin wani kamfani a Faransa da ya bullo da "manhajar leken asirin kwamfyuta" bayan ya ce ana iya amfani da ita wajen "gano ko ɗanka yana luwaɗi".

Da yake ba da "haske", kamfanin mai suna Fireworld ya nuna cewa "yin kutse shafinsa na Facebook" don ganin ko yana ziyartar shafukan 'yan luwadi ka iya tabbatar wa iyaye zargin da suke da shi.

Sai dai tuni kamfanin ya janye wannan bayani.

Wata kungiyar kare hakkokin 'yan luwadi da madigo ta matasan Faransa ce ta yayata rubutun na wannan kamfani.

Sakatariyar tabbatar da daidaito ta Faransa, Marlène Schiappa ta sake tura sakon twitter da kungiyar ta aika game da rubutun kamfanin Fireworld, inda ta yi sharhi da cewa hakan ya nuna cewa "kyamar 'yan luwadi da nuna bambanci tsakanin mace ko namiji sun yi zurfi. Kuma gaba daya za mu yake su".

A cikin bayaninsa na intanet, wanda tuni aka cire, kamfanin ya ce "iyali ginshikin al'umma ne. Don haka halayyar jima'in 'ya'yanka, ita ce tushe kai tsaye ga ci gaban rayuwar iyalinka, kuma hakan na da matukar muhimmanci gare ka".

Rubutun ya ci gaba da zayyana bayanai kan hasken da iyaye ka iya gani su yi zargin cewa ko 'ya'yansu na halayyar neman maza. Sai dai rubutun bai ce komai game da batun mata ba.

Bayanan sun hadar da "tsananin damuwa da kyawunsa", da sha'awar karance-karance da zuwa gidan raye-raye fiye da kwallon kafa, zama mai matukar shayi a matsayinsa na matashi, yin huji don kwalliya da yawan son mata mawaka.

Daga nan sai ya ba da shawarar wasu hanyoyi don tabbatarwa, ciki har da "bibiyarsa a Facebook", don ganin "ko yana ziyartar shafukan 'yan luwadi" da "leken asirin sakwanninsa na kashin kai".

Hakkin mallakar hoto FIREWORLD
Image caption An cire ainihin wannan bayani daga shafin intanet na Fireworld

Sai dai a martanin da ya mayar ga kungiyar L'Amicale des jeunes du Refuge, Fireworld ya rubuta cewa "babbar manufar buga wannan bayani ita ce bunkasa hanyoyin binciko bayanai a intanet, don haka ba a yi shi don mutane su karanta ba".

Haka kuma, wani sakon imel na kamfanin ya ce: "Muna nadamar rashin yin tsokaci kan abin da zai je ya zo game da wannan rubutu...Muna neman afuwar duk wadanda muka batawa."

Sai dai, shafin intanet din Fireworld na Ingilishi ya nuna a yanayi irin daban-daban, da wani mai saye ka iya son bibiyar harkokin wani a kwamfyutarsa, ciki har da "don iyakance harkokin matashin danka a kwamfyuta" da duba "abin da ma'aikatanka suke yi" gami da "bin kwakkwafin wani cin amana a zamantakewar aure ko wata mu'amala".

Labarai masu alaka