Yara na cikin bala'in yunwa da cutar kwalara a Yemen

Yemen
Image caption Jarirai da aka haifa cikin yakin, ba sa samun isasshen nonon uwa da zai gina musu jiki, wasu daga ciki cutar Tamowa ta kama su

Shekara biyu da aka kwashe ana yaki a kasar Yemen, ya janyo karancin abinci, da magunguna, yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar taimako.

Wakiliyar BBC Nawal al-Maghafi ta niki gari har kasar ta Yemen, don ganewa idonta halin da kasar ke ciki, a daidai lokacin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ke ci gaba da luguden wuta a wasu sassan kasar da nufin yaki da 'yan tawaye na kabilar Houthi kuma mabiya darikar Shi'a.

Nawal ta fara cin karo da wata uwa da ke cikin halin dimuwa da damuwa, ga tsananin wahala da rashin abinci ga kuma rashin lafiyar da 'yarta ke fama da ita.

Sunan matar Samira, ta kuma shigo cikin wata makaranta da gudu, wadda a halin da ake ciki ta zama dan karamin asibitin da ake kwantar da wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa.

Kana kallonta za ka san tana cikin tashin hankali, irin wanda iyaye ke shiga a lokacin da 'ya'yansu ba su da lafiya, da kuma kokarin tabuka wani abu da nufin ceton ransu.

Samira ta yi tafiya mai tsawo kafin ta iso asibitin, tafiya ce a wahala da kafa cikin gudu-gudu, da sassarfa saboda ba ta da wani zabi baya ga hakan tun da babu abin hawan da za ta yi amfani da shi don kawo dan nata asibiti.

Da azama ta dora 'yarta mai suna Orjowan 'yar wata 18 kan teburin da ke gaban likitocin da ke wurin, tare da rokon su taimaka kar 'yar ta mutu. Kwayar idonta kadai ta isa ba ka amsar a wahale take, ta kuma gaji.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli bidiyon yadda yunwa da kwalara ke hallaka yara a Yemen

Hakika Samira ta kai labari cikin shekaru biyun da aka kwashe ana yaki, babu kwanciyar hankali, ba mataimaki sai Allah da kyar ake samun cin abincin da ya sawwaka shi ma ba kullum ba.

Yakin da ba a san lokacin da zai kare ba, da ka kalli Orjowan za ka san ta wahala, idanunta sun fito waje, ta rame, sannan idan aka dorata a sikelin auna nauyi ba na jin za ta yi nauyin abin a zo a gani, kasusuwa sun fito a kirjinta kamar za ka kirga su saboda tsananin rama ga kuma rashin kuzari.

Tsananin yunwa, da rashin kwanciyar hankali da uwa uba cutar kwalara da ta barke a kasar Yemen, ta sanya iyalai da dama cikin halin ni 'yasu.

Image caption Rashin abinci mai gina jiki, da tsaftataccen ruwan sha na daga cikin matsalolin da yara kanana ke ciki a Yemen

Kamar sauran 'yan kasar kusan miliyan uku, ita ma Samira da 'yan uwanta yakin ya daidaita musu muhallahi. Wani jirgi maras matuki da kawancen Saudiyya ke jagoranta shi ne ya afkawa gidansu.

'Ya'yan mutane kamar na Samira, kusan 500,000 ne 'yan kasa da shekara biyar ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Samira ma na daga cikin matan da dan abincin da suka ci bai kai yawan da zai ba su wadataccen ruwan nonon da za su shayar da jariransu ba.

Abin tausayin shi ne, Samira na bai wa 'yarta madarar gari da aka dama da ruwan da ba shi da wata cikakkiyar tsafta wanda shi ya haifar mata da cutar amai da gudawa.

Ta yanke jiki ta fadi kan gwiwarta cikin matsanancin kuka ta fara magana, "Na yi duk kokarin da zan yi don na ceci 'yata daga fadawa wannan halin, duk kokarin da na yi na neman taimako abin ya gagara, dan uwana da na nemi taimako a wurinsa ba zai iya min komai ba saboda shi ma yana cikin wani mawuyacin hal."

Orjowan ta kurawa mahaifiyarta ido, ta galabaita har ma ba za ta iya kuka ba, ta kara dashewa tamkar babu jini a jikinta, jikinta ya kara saki saboda rashin kuzari.

Labarin Samira daya ne daga cikin abubuwan da wakiliyar BBC ba za ta taba mantawa da su ba a ziyarar da ta kai kasar Yemen, a daidai lokacin da yaki ya daidaita kusan rabin kasar.

Kara shiga cikin Yemen, da ziyartar garuruwa da haduwa da mutanen da ke cikin mawuyacin hali, wani abu ne da bai taba gushewa a idanun wanda ya gani ba.

Mutane na cikin halin kunci, da rashin abinci, babu magani, kusan ba su da komai da za su yi tinkaho da shi, kasar ta zama kamar Kufai.

Yayin da Nawal ta isa yankin arewacin Yemen wurin da 'yan tawaye ke iko da shi, sun shiga kusan duk kananan asibitocin da ke yankin da suka ziyarta, akwai marasa lafiya da yawa suna fama da cutar amai da gudawa.

Nawal ta ce ta ga wasu iyalai su 18, baki dayansu suna fama da cutar amai da gudawa, to amma ta su matsalar da sauki don kuwa sun samu damar zuwa asibiti a kan lokaci duk kuwa da wahalar da suka fuskanta amma kwalliya ta biya kudin sabulu.

An yi kiyasin kusan mutum 2000 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara, kuma shi ne adadi mafi girma da cutar ta dauki ran mutane a duniya. Kuma wasu mutum 540,000 ne suka kamu da cutar.

Yakin da ake ciki, ya sanya an rufe kusan rabin cibiyoyin lafiya da asibitoci da ake da su saboda rashin kayan aiki, yayin da sama da muum miliyan 15 ne ba su da halin zuwa sibiti.

Da tawagar da wakiliyar BBC ke ciki ta sake nausawa cikin kasar, sai da suka yi tafiyar kusan sa'a biyu kafin suka ga wani asibiti. Duk gidan da suka shiga da asibitoci mutane ne yashe a kasa da ke fama da cutar kwalara.

Wani mutum mai suna Abdallah da kanwarsa Hindi, cikin gajiyawa sun shaida wa tawagar dalilin da ya sa ba su je asibiti ba, rashin kudi da hanyar da za a dauki marasa lafiyar tare da bakin talaucin da yakin ya jefa su a ciki ne ya hana su fita.

Image caption Gabar tekun Aden, da ake shigo da kayan abinci kafin fara yakin Yemen

Yawancin kayan abincin da kasar ke amfani da su, daga kasashen waje ake shigo da su kuma ana amfani ne da tashar jirgin ruwa ta Hudaydiya, wanda kuma luguden da Saudiyya ke yi ta sama ya daidaita wurin babu wani abinci da ake iya shigowa da shi.

Yawancin 'yan kasar sun dogara ne da tallafin da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji ke kai musu. Mata da kananan yara, da tsofaffi su ne suka fi shiga mawuyacin hali a shekarun da aka kwashe ana yakin.

Kalilan daga ciki ne suka yi kaura wasu kasashen, wadanda ke kasar sun ce babu inda za su je saboda ba su da wurin da ya fi kasarsu.

Duk da cewa akwai tarin masu karamin karfi a kasar Yemen, amma talaucin bai musu kanta ba idan aka kwatanta da lokacin da ake zama lafiya da lokacin yaki.

A yayin da ake gab da shiga shekara ta uku da fara yakin, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen duniya su kawo wa Yemen da al'umar da ke cikinta daukin mummunan halin da suke ciki.

A bangare guda kuma, an yi kira ga bangarorin da ke rikici a kasar su hau teburin sulhu don kawo karshen halin kunci da bakar wahalar da 'yan Yemen ke ciki.

Image caption Yawancin iyalai sun dogara ne ga tallafin kasashen waje

Labarai masu alaka