Qatar da Iran sun kulla kawancen diflomasiyya na kut-da-kut

An Iranian woman walks past a Qatar Airways office in Tehran on 6 June 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iran ta yardar jiragen kasar Qatar su yi amfani da sararin samaniyyanta yayin da take taddama da Kasashen Larabawa.

Kasar Qatar ta dawo da huldar diflomasiyya da kasar Iran a wani mataki na bijire wa bukatar da Kasashen Larabawa hudu suka yi mata na yanke hulda da kasar.

Hadaddiyyar Daular Larabawa ta bukaci jakadanta ya koma gida a shekarar 2016 lokacin da aka kai hari a ofishin jakadancin Saudiyya a Iran, biyo bayan matakin da Saudiyya ta dauka na zartar wa wani malamin Shi'a hukuncin kisa.

Amma a yanzu kasar tana kokarin fadada yawan kasashen da take hulda da su.

Iran ta taimakawa Qatar da taimakon abinci da kayayyaki yayin da makwabtanta suka kakaba mata takunkumi a watan Yuni.

Kasashen Saudiyya da Hadaddiyyar Daular Larabawa da Masar da kuma Bahrain suna zargin Qatar da taimaka wa ayyukan ta'addanci da kuma yadda take dasawa da Iran.

Sai dai Qatar ta musanta duka zarge-zargen.

Ko da yake, Qatar ba ta bayyana lokacin da jakadanta zai koma aiki Iran ba. Amma sanarwar dawo da huldar ta zo ne bayan da Ministan Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ya yi magana da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif ta waya.

Mutanen biyu sun tattauna harkokin kasashen biyu ne da kuma hanyoyin da za su bunkasa su, kamar yadda wata sanarwa ta ce.

Sai dai ba a tabo batun takaddamar da ke tsakanin Qatar da makwabtanta hudu ba.

Labarai masu alaka