Nigeria za ta fara taso keyar masu laifin da suka gudu UAE

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto TWITTER

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wata yarjejeniyar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda za ta fadada yaki da cin hanci da gwamnatinsa take yi da tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Yarjejeniyar ta yi tanadin musayar mutanen da suka aikata manyan laifuka tsakanin Najeriya da Hadaddiyyar Daular Larabawa.

Shugaban ya bayyana al'amarin da wani muhimmin ci gaba ga kasar wanda zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci da ciki da wajen kasar.

Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tasa keyar wadanda aka samu da laifin aikata cin hanci a kasashen biyu.

Ya ce an jinkirta fara aiki da cikakkiyar yarjeniya ne saboda bangarorin biyu ba su kammala cimma matsaya ba.

"Wannan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma zai taimaka wa hukumomin kasashen wajen gurfanar da wadanda aka samu da aikata laifin cin hanci da rashawa," in ji Shugaba Buhari.

Sauran batutuwan da shugaban ya zartar a ranar Alhamis har da wata yarjejeniya da ta shafi yankin Tafkin Chadi da Kamaru da Janhuriyar Tsakiyar Afirka da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar.

Labarai masu alaka