Takaddama ta kaure tsakanin malamai kan ranar Sallah a Niger

Sallar idi a Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images

A Jamhuriyar Nijar yanzu haka wata takaddama ta taso bayan da majalisar malaman kasar ta bayar da sanarwar tsayar da ranar Asabar 11 ga watan nan na Zul Hijja a matsayin ranar sallah babba.

Sai dai wasu kungiyoyin addini musulmi sun ce ba su amince da wannan mataki ba, saboda Saudiyya za su yi arfa ranar Alhamis wanda bai zamo daidai ga wani bangare na duniya kuma su yi idi ba bayan kwana biyu da hawa arfa,

Ga dai rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko mana da Nijar din:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Tchima kan takaddamar ranar sallah

Labarai masu alaka