Kalli bidiyon yadda yunwa da kwalara ke hallaka yara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon yadda yunwa da kwalara ke hallaka yara a Yemen

Harin bama-baman da ake kai wa tashar jiragen ruwa ta Hudadyah a Yemen ya jawo matsalar rashin shiga da kayan abinci da sauran kayayyakin bukatun rayuwa kasar.

Tawagar BBC ta kai ziyara kasar don ganin yadda ma'aikatan lafiya ke ka-ka-ni-ka-yin taimakon masu fama da cuta, a kasar wacce ke fama da rashin abinci da wutar lantarki.