Facebook barazana ne ga Dimokradiyya - Jon Snow

Asalin hoton, PA/Getty Images
Jon Snow, Mark Zuckerberg
Mai gabatar da shirin Joh Snow, ya ce kamata ya yi Facebook ya dauki mataki kan yada labaran da ba su da tushe balle makama, ya kuma samar da sahihiyar kafar yada labarai mai inganci.
Tsohon dan jaridar da ke gabatar da labarai tun a shekarar 1989, ya gabatar da wata kasida a bikin kalankuwar talabijin, inda ya ce shafin Facebook na yi wa Dimukradiyya barazana saboda abubuwan da ya ke yadawa.
Sai dai mamallakin Facebook din wato Mark Zuckerberg, ya ce kamfaninsa na taimakawa kafafen yada labarai.
'Abin da ya kamata a yi'
Cikin jawabin da ya dauke shi minti 50, Mista Snow ya ce, Facebook ya taimaka tare da janyowa Channel 4 karin mutanen da ke bibiyar labaran da suke yadawa, sai dai masu wallafe-wallafe na fama da masu bibiyar shafukan sada zumunta.
Ya kara da sukar lamirin kamfanin, da ya yi zargin yana yada labaran karya. Ya kuma ce shafin Facebook shi ya sanya wani labarai da ke cewa ''Paparoma ne ya daurewa Donald Trump gindi ya zama shugaban Amurka'', alhalin sam labarin ba haka yake ba.
"Sai dai hakan ya janyo sama da mutane miliyan daya suka yi ta tofa albarkacin bakinsu a lokacin zaben shugaban Amurkar, duk da cewa labarin ya shahara amma ta inda ya fito shi ne abin dubawa.
''Don haka Facebook yana da jan aiki a gabansa, don yin tankade da rairaya tare da kaucewa yada labaran karya'' in ji Mista Snow.
Asalin hoton, PA
Jon Snow kenan a lokacin da ya ke gabatar da kasidar a Edinburgh
Ya kara da cewa Facebook na biyan masu wallafa masa labarai don kudi kalilan kan duk labaran da aka samu, wanda dan abin da ake ba su bai taka kara ya karba, ba kuma zai biya su wahalar da suka sha wajen samar da labaran da za su tabbatar da sahihancinsu da kuma bincike irin wanda 'yan jarida ke yi ba.
Tashar BBC ta Channel 4 ta wallafa cikakkiyar kasidar da Snow ya gabatar.
Mayar da martani
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
A ranar Laraba ne mamallakin kamfanin Facebook Mista Zuckerberg ya ce suna kokari don tantance labaran da suke yadawa, da muka inganta albashin ma'aikata.
A martanin da ya mayar da kuma ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce a daidai lokacin da mutane da dama ke samun labarai a shafin sada zumuntar daga sassa daban-daban na duniya, suna kokarin kawo daidaito da inganta labaran da suke wallafawa.
Zuckerberg ya kara da cewa za a samar da wata hanya da mutane za su dinga duba dukkan labaran da shafin ke yadawa, don tabbatar da sahihancinsa.
Ya ce manufar sauye-sauyen da suke son kawowa ita ce tantance labaran gaskiya da na karya, ga duk wanda ya kawo labari za a dinga sanya tambarinsa a kasan labarin yadda idan an samu matsala shi za a tuntuba dan ya kare kansa kan labarin da ya wallafa.
''Bai wa mutane damar yin magana ba shi kadai ne abin da ake bukata ba, ana bukatar samar da wata kungiya da aikinta baki daya shi ne tankade da rairayar labarai.
Za mu kara samar da wasu hanyoyin don taimakawa bangaren watsa labarai, sannan masu dauko rahotanni da masu wallafawa za su yi aikin su yadda ya kamata,'' in ji Zuckerberg.
Sai dai abin da ya wallafa din, ba wai yana maida martani ko sukar lamirin Mista Snow ba ne.
Tun da ko a lokacin da yake gabatar da kasidar, Mista Snow ya ce yana daya daga cikin masoya shafin sada zumunta na Facebook.
Ya ce, ''Shafin Facebook yana da dadin mu'amala, a wasu lokutan kuma bashi da maraba da mummunan mafarki.
"Ba na daga cikin mutanen da suke saurin bayar da kai bori ya hau.''
Fake news - is Facebook moving fast enough?
The social network plans to educate users about fake news - but will it make a difference?