Me ya sa jiragen sojin Nigeria ke yawan hatsari?

Jirgin sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jirgin sojin Najeriya

A ranar Alhamis ne wani karamin jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Kaduna da ke arewacin kasar, a lokacin da yake wani aiki.

A wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta aikewa manema labarai ta ce, matukin jirgin wanda shi kadai ne a ciki lokacin da hatsarin ya afku ya mutu.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo hatsarin ba, amma tuni hafsan sojojin sama na kasar ya bayar da umarnin kafa kwamitin bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin.

Wannan hatsari dai a cewar sanarwar, tuni ne kan yadda aikin tukin jirgin sama ke da matukar hadari.

Rundunar sojin saman ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin, wanda ya kasance kwararren matukin jiragen yakinta ne da ya san aikinsa.

Labarai masu alaka